✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kai hari gidan dan majalisa sun dauke mutum 2 a Katsina

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari gidan dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Kusada, Kankiya da…

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari gidan dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Kusada, Kankiya da Ingawa a jihar Katsina, Abubakar Yahaya Kusada tare da sace mutum biyu.

Kusada dai tsohon Kakakin Majalisar Dokokin jihar Katsina ne kuma yanzu dan majalisa mai wakiltar yankin a Majalisar Dokoki ta Kasa.

Wata majiya ta shaidawa Aminiya cewa, “Da misalin karfe daya na daren ranar Asabar, ’yan bindigar suka yi wa gidan dan majalisar tsinke tare da yin awon gaba da ’yan aikin gidan mutum biyu, wata mata mai suna Talatu da wani matashi mai suna Suleiman.”

Kazalika, wata majiyar ta ce tun da farko dai maharan da ake zargin masu garkuwa ne domin neman kudin fansa sun nemi a nuna musu mahaifiyar dan majalisar wacce aka shaida musu ba ta nan.

“Daga nan ne suka dauke mutum biyun, wadanda dukkansu ke da kusanci da dan majalisar,” inji majiyar.

A wani labarin kuma, wasu ’yan bindigar sun kai hari kan wasu masu aikin kato-da-gora a karamar hukumar Kurfi tare da hallaka mutum uku.

Mazauna yankin sun ce in banda daukin da jami’an tsaro suka kai, adadin wadanda aka hallaka din na iya wuce ukun.

Bugu da kari, shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Sabuwa ya rasu ranar Juma’a.

Marigayin ya rasu ne bayan raunukan harsasan da suka same shi yayin harin da ’yan bindigar suka kai kauyensa na Labi, makonni biyu da suka wuce inda suka hallaka mutum uku.

Sai dai ya zuwa lokacin hada wannan rahoton. Rundunar ’Yan Sandan jihar ba ta kai ga tabbatar da rahotannin ba.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isah ya ce yana bukatar yin kiraye-kiraye a waya kafin ya tabbatar da Su.