✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindigan Zamfara sun fi jami`an tsaro makamai- Yari

Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya bayyana cewa, ‘yan bindigan da suke fashi da makami a jihar suna da makamai fiye da sauran jami’an tsaron…

Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya bayyana cewa, ‘yan bindigan da suke fashi da makami a jihar suna da makamai fiye da sauran jami’an tsaron jihar.

Rahotanni na bayyana cewa, a shekaru biyar da suka shude jihayr Zamfara na fuskantar barazanar ‘yan bindiga inda aka kashe dubban jama’ar jihar, yayin da garkuwa da jama`a ya zama ruwan dare a jihar.

A yayin da Gwamna Yari ya gana da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa Abuja, ya bayyanawa manema labarai cewa, a cikin daya daga moboyar makaman `yan bindigar sun gano sama da bindigogi 500 kirar AK-47.