✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindigar Zamfara sun koma satar shanu

A ’yan kwanakin nan ’yan bindiga a Jihar Zamfara sun kai hare-hare a kauyen Sunke da ke Karamar Hukumar Anka, inda suka hallaka sojoji tara…

A ’yan kwanakin nan ’yan bindiga a Jihar Zamfara sun kai hare-hare a kauyen Sunke da ke Karamar Hukumar Anka, inda suka hallaka sojoji tara tare da raunata wadansu da dama.

Harin dai na zuwa ne duk da kulla yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi da su a watan Yunin da ya gabata. Sababbin hare-haren dai sun tada hankalin al’ummar jihar, musamman mazauna karkara.

Kafin harin na makon jiya, an ga ayarin ’yan bindigar a kan babura a wani gari mai suna Mayanci da ke kan babban titin da ya hada Gusau da Sakkwato.

Duk da yake dai ’yan bindigar ba su kashe kowa ba amma shaidu sun ce ’yan bindigar sun rufe babban titin na Gusau zuwa Sakkwato na wani dan lokaci, kafin su bar masu ababen hawa su ci gaba da wucewa ba tare da wani bata lokaci ba.

To amma shaidun sun ce ’yan bindigar sun rika shiga shagunan jama’a da ke bakin titin kuma suka rika dibar kaya suna tafiya ba tare da biyan kudi ba. Kai har ma wani gidan mai suka shiga kuma suka sha mai suka tafi abinsu ba tare da sun biya ba.

’Yan bindigar kuma sun shaida wa jama’ar garin cewa kowa ya kwantar da hankalinsa, su ba su zo da nufin kashe kowa ba, hasali ma suna kan hanyarsu ta zuwa Birnin Gwari ne da ke Jihar Kaduna. Haka dai suka ci karensu ba babbaka a wurin kafin su hau baburansu su tafi.

Mako guda bayan faruwar lamarin, sai aka samu labarin cewa ’yan bindigar sun kashe sojoji tara a Karamar Hukumar Anka. Maharan dai sun yi wa sojojin kwanton bauna ne kuma suka bude musu wuta, sai dai su ma maharan rahotanni sun ce sun yi asarar mutanensu da dama.

Wani babban jami’in gwamnati da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa ’yan bindigar sun kai harin ramuwar gayya ce bayan da sojojin suka rika yin dauki-daidai a kan gungun ’yan bindigar da suke zargin cewa barayin shanu ne.

Wani mazaunin yankin mai suna Muhammad Aliyu Kawaye ya shaida wa Aminiya cewa hankalin mazauna yankin ya tashi bayan da suka ga sojojin da aka girke a yankin suna janyewa. Ya ce suna cikin halin rashin tabbas na abin da zai faru.

“Mutane da dama suna barin garin namu na Kawaye suna tafiya wajen garin Bagega saboda sojojin da aka girke sun janye kuma sun fada mana cewa za su dawo idan aka kara yawansu. Yanzu haka maganar da nake da kai mutane musamman mata da yara suna ficewa daga garin,” inji shi.

Ya ce duk da cewa an yi sulhu da ’yan bindigar, amma rahotanni sun ce ba su daina satar shanu da cin zarafin matan jama’a ba, sai dai sun daina kashe mutane da garkuwa da su don karbar kudin fansa kuma jama’a suna zuwa gonakinsu da kuma wasu wuraren da a baya ba su iya zuwa.

Ya ce sun samu labarin cewa suna shiga garuruwa suna kora shanu da sauran dabbobi, wani lokaci ma sukan ci zarafin mata. Ko a lokacin da suka kashe sojojin da ke Sunke, an ga ’yan bindigar da daruruwan shanu da ake zargin na sata ne.

“Garuruwan Gobiriwa, Tungar Daji, Dawan Jiya da kuma Duza na daga cikin wadanda suka yi asarar dabbobinsu saboda addabarsu da ’yan bindigar suka yi a ’yan watannin nan. Kiwo dai a wuraren ya zama abu mai matukar wahala. Hatta su kansu Fulanin da ke kiwon shanun a dajin matukar ba cikin kungiyarsu suke ba, dabbobinsu ba su tsira ba, kuma suna tafiya da shanun suna cinye amfanin gonar da duk suka yi karo da shi. Kuma ba su damu da barnar da suke yi wa jama’a ba,” inji shi.

Shi ma wani mazaunin yankin mai suna Kabir Ashiru ya shaida wa wakilinmu cewa, ana zargin cewa ’yan bindigar da suka kashe sojojin ba wadanda aka yi sulhu da su a Zamfara ba ne, sun zo daga dajin Birnin Gwari. Haka kuma dama can suke addabar jama’ar yankin.

To amma binciken da Aminiya ta yi ya nuna cewa in ban da Karamar Hukumar Anka babu rahoton kai hari a wani sashi na jihar. Kuma an samu daukewar kai hare-hare da kuma garkuwa da mutane tun bayan kulla yarjejeniyar sulhu da ’yan bindigar.

Da Aminiya ta tuntubi Mai ba Gwamna Bello Matawalle na Zamfara shawara ta fuskar tsaro, Alhaji Abubakar Dauran, ya shaida wa wakilinmu cewa yarjejeniyar da aka kulla da ’yan bindigar tana nan daram.

“Kuma game da satar shanu, ana daukar matakin da ya kamata. Shugabannin tubabbun ’yan bindigar na yankuna daban-daban sun shaida mana cewa za su ci gaba da sa ido a kan yaransu, domin wadanda suka kashe sojoji baki ne daga wani wuri suka shigo jihar,” inji shi.

Ya kara da cewa; “Kazalika, daya daga cikin abin da aka cimma a wajen taron shi ne su shugabannin bangarorin tubabbun ’yan bindigar za su fara karbar makamai daga wurin yaransu tun daga jiya Alhamis.”

Da yake magana kan tubabben dan bindigar nan da ake kira Dogo Gide, Abubakar Dauran ya ce Dogo Gide, wanda yanzu yake yankin Rijau a Jihar Neja ya ba su goyon baya lokacin da suke zaman sulhu da ’yan bindigar.

“Dogo Gide ya turo wakilansa kuma ya ce yana goyon bayan sulhu kuma shi ya daina fashi da garkuwa da jama’a, shi ne ma dalilin da ya sa ya bar yankin Zamfara zuwa Jihar Neja, don ya ci gaba da kiwon shanunsa.

Daga karshe, ya yi kira ga mutanen jihar su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa gwamnati tana daukar dukkan matakai na tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi. Sa’anan ya bukaci jama’a su kai rohoton duk wani ko kuma wata kungiya da suke da shakku a kanta ga jami’an tsaro don daukar mataki.