✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Birtaniya 8 sun isa Instanbul a keke a hanyarsu ta zuwa Hajji

Wavansu Musulmi ’yan Birtaniya su takwas, sun isa birnin Instanbul na kasar Turkiyya a ranar Asabar don yada zango, a hanyarsu ta zuwa sauke farali,…

Wavansu Musulmi ’yan Birtaniya su takwas, sun isa birnin Instanbul na kasar Turkiyya a ranar Asabar don yada zango, a hanyarsu ta zuwa sauke farali, a wata dtafiyar da suka faro daga birnin Landan na Birtaniya a kan kekuna don isa Madina birni na biyu a daraja a Musulunci. Kamar yadda kafar labarai ta Anadolu ta Turkiyya ta ruwaito.

Kafar labaran ta ruwaito vaya daga cikin matafiyan, Zain Lambat, yana cewa: “Wannan tafiya ce mai matukar muhimmmanci ta hanyoyi da dama. Dukkanmu mun kamo hanyar ce; saboda addininmu. Mun kuma havu da mashahuran mutane a yayin tafiyar; akwai labarai da daman gaske game da tafiyar. Godiya sosai ga irin muhimman lokutan da muka samu na damar shiga wurare da daban-daban.”

Rukunin mutanen da suka kira kansu, “Masu Rangadin Zuwa Hajji,” sun faro tafiyar ce tun ranar 7 ga Yuni, kuma ana sa rai za su shafe kwana 60 kan hanyar tasu.

Sun tsara yin tafiyar a kan kekuna inda za su ratsa kasashe 17, yayin da za su yada zango don tsallakawa kasar Syria da Iraki su isa Masar ta jirgin sama.

Suna dai hakilon favakar da jama’a tare da neman tara kuvave don tallafa wa Musulmin duniya mabukata da nufin gina masallatai da makarantu.

“Mun faro tafiyar ce a ranar 7 ga Yuni, daga birnin Landan a kan kekunanmu. Mun tsara isa birnin Madina, bayan mun yi tafiyar kilomita dubu huvu, (Mil 2,485) a kan kekuna a tsawon kwana 60 cur,” inji vaya daga cikin matafiyan, mai suna Junaid Afzal.

Ya ci gaba da cewa: “Muna hankoron tara Dala dubu 628 da 600, don taimaka wa al’ummar Musulmi wajen gina masallatai da makarantu.”

Mista Afzal, ya shawarci jama’a da rika zuwa Hajji a kan kekuna, yana mai cewa: “Abin bisa ravin kanka ne kawai…… A cikin Alkur’ani Mai girma, Allah Mavaukakin Sarki Ya ce: “Idan Ya yi nufin faruwar al’amari; kawai sai Ya ce kasance; kuma sai ya wanzu.” Hakan ya kamata mutane su fuskanci rayuwa.”.

Zain Lambat, ya nuna godiya ga Turkawa, inda ya ce, sun karbe su da hannu biyu a birnin Instanbul. “Duk inda muka je, akwai masallatan Turkawa; kuma mun havu da ’yan uwanmu Turkawa, sun nuna mana matukar karamci,” inji shi.

“Idan kana da kyakkyawar niyyar sauke farali, to Allah Zai saukake maka hanyar haka… Mun faro tafiyar ce da karamin guzuri; amma Allah cikin ikonSa, sai Ya hava mu da mutane nagari yayin tafiyar; wavanda suka yi ta tallafa mana,” inji Lambat.

An taba samun masu makamancin wannan tafiya, don gudanar da aikin Hajjin, inda ko a watan jiya, an samu wavansu mahaya kekuna su huvu ’yan kasar Kenya tare da taimakon wavansu mutum biyu, da suka kaddamar da tafiya mai tsawon gaske daga birnin Nairobin Kenya zuwa birnin Makka, da zimmar sauke faralin tare da tara kuvave don ilimintar da mabukata kananan yara ’yan kasar Kenya.

A shekarar 2018, wavansu iyali Musulmin kasar Indonesiya biyar, sun sabi tafiya mai nisan kilomita dubu 13 zuwa Makka a kan kekuna, don sauke faralin.

Sa’annan a shekarar 2017, an samu wani van kasar Indonesiya, wanda ya yi tattakin kilomita dubu 9 don yin aikin Hajjin.

A shekarar 2012 kuma, an samu wani Musulmi van kasar Bosniya, mai suna, Senad Hadzic, mai shekara 47,  wanda shi ma ya taka sayyada zuwa birnin Makka don sauke farali. A yayin tattakin nasa, mutumin ya yi tafiya mai tsawon kilomita dubu 5 da 900 (kimanin mil 3,600) daga kauyensu a kasar Bosniya zuwa birnin Makka.

A kowace shekara Musulmi daga sassan duniya na zuwa birnin Makka, don yi aikin Hajji, wanda rukuni ne daga cikin rukunan Musulunci biyar. Aikin Hajjin ya kunshi gudanar da ibadu iri-iri da suke wajabai a addinin Musulunci; tare da tuna wasu  jarrabawar da Allah Mavaukakin Sarki Ya jarabci bawanSa Annabi Ibrahim (AS) tare da iyalansa masu tsarki.

Kowane lafiyayyen Musulmi baligi, kuma mai halin zuwa Hajji; to dole ne a kansa, ya sauke faralin akalla sau vaya a rayuwarsa.