✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Boko Haram sun kashe manoma 8 a Borno

Mayakan Boko Haram sun kashe manoma 30 a Konduga, Jihar Borno

Akalla mutum takwas ne maharan Boko Haram suka aka kashe a harin da suka kai a gonakin da ke kusa da Maiduguri, cikin Karamar Hukumar Konduga, Jihar Borno.

Da yake tabbatar da hakan, Mai Garin Ngimtilo, Lawan Bunu Bukar ya ce sama da mutum 30 sun bace tun makon jiya, kuma har yanzu ba a ji duriyarsu ba.

“Abun bakin ciki, mun sanar da sojoji cewa ’yan Boko Haram sun kashe mana mutane kusa da Tirela Park a Karamar Hukumar Konduga amma suka ki zuwa, sai da safen nan ’yan CJTF suka je kwaso gawarwakin.

“An fara kawo harin mako daya da ya wuce, kuma akalla manoma 30 sun bata.

“Yanzu muka binne mutum shida da aka kashe a wani kauye ranar Asabar, ana zana’izar wasu a wani bangare cikin gari kuma an sace mutum shida a cikin gonakansu.

“A kullum za a bar mu muyi noma amma da lokacin girbi ya yi sai Boko haram sun rinka kai mana hari a gonakan, su kashe mu ko su sace mutane. “Abun haushi tafiyar ba ta fi kilomita biyu ba daga cikin gari”, inji shi.

Bukar ya roki gwamnati da ta kai musu dauki saboda mutanensu na cikin bala’i.

Aminiya ta ruwaito cewar hare-haren da ake kai wa manoma sun zama ruwan dare kuma mutane kauyuka ba sa iya tafiyar da ta fi kilomita biyar daga cikin kauyukan ba tare da ’yan Boko Haram sun salwantar da su ba.