✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bumburutu na cin karensu ba babbaka a Abuja

’Yan bumburutu na ci gaba da cin karensu ba babbaka, inda suke sayar da kowace lita a kan Naira 250 zuwa Naira 300 sakamakon karacin…

’Yan bumburutu na ci gaba da cin karensu ba babbaka, inda suke sayar da kowace lita a kan Naira 250 zuwa Naira 300 sakamakon karacin man da ake fama da shi a ciki da kewayen Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Wakilin Aminiya da ya zagaya sassan birnin ya gane wa idonsa yadda ’yan bumburutun ke kai-komo suna sayar da man ga masu motocin da suke mutukar bukata.

Aminiya ta gano cewa ’yan bumburutun na sayar da galan mai cin lita hudu a kan Naira dubu daya da dari biyar sannan galan man mai cin lita takwas a kan Naira dubu uku.

Wani dan bumburutu da Aminiya ta tattauna da shi mai suna Aminu Isa da ke sayar da man a kan titin Mabushi, ya bayyana cewa dole ce ta sa suke sayar da man da tsada.

“Mu ma da sai mun sha wahala sannan muke samun man. Ka ga dole mu ma mu sayar da man da tsada don mu fanshe wahalar da muka sha kafin mu samu a gidan mai,” inji shi.

Shi ma Auwalu da ke sayar da man a yankin Kucigoro da ke kan titin filin saukar jiragen sama na Abuja, ya ce sai sun bayar da cin hanci kudi mai yawa sannan suke samun man a gidajen mai.

“Idan muke je gidan mai sai mun bai wa masu zuba man cin hancin kudi masu yawa sannan su ba mu man. Shi ya sa mu ma muke kara kudi domin mu fitar da ribarmu,” inji shi.

Ya bayyana cewa suna bai wa masu zuba man Naira dubu daya a duk lita 20 da suka zuba musu. Sai dai wani mai sayar da mai a gidan mai na NIPCO da ke kan titin filin saukar jiragen sama na Abuja, wanda ya ki bayyana sunansa ya karyata zargin da ’yan bumburutun suka yi.

Ya ce hukumar gidan man ta ba su dokar kada su rika zuba wa masu babur da jarkoki.

Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin hukumar lura da gidajen man ta DPR ya ci tura. Amma wani ma’aikacin hukumar da bai so a bayyana sunansa ba saboda ba shi da hurumin yin magana da manema labarai, ya bayyana cewa hukumar na mutukar kokarinta don ganin cewa gidajen mai sun bin doka da oda.