Da Dumi Dumi

‘Yan daba sun kona Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP

PDP-logo

Wadansu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne sun kone Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP ta Karamar Hukumar Ofu dda ke Jihar Kwara, Misis Acheju Abuh a gidanta da ke unguwar Ochadamu.

A ranar Litini da ta gabata ce ’yan dabar da ake zargin magoya bayan jam’iyya mai mulki APC ne suka hallaka ta. ’Yan dabar sun shiga cikin gidan matar da misalin karfe 2 na rana, inda suka rufe hanyoyin shiga ko fita. Suka watsa fetur a gidan tare da kunna wuta.

An ce ’yan dabar sun hana mutane kai wa matar taimako sakamakon harbin da suka rika yi da bindigogi  wanda hakan ya sa mutane suka gudu.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kogi, William Aya, ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce, sun samu rahoto  daga wani mutum a Karamar Hukumar Ofu da misalin karfe 4:30 na yamma.

Gawar matar na dakin ajiye gawarwaki na Asibitin Koyarwa na Anyigba don bincike. Tuni ’yan sanda da jami’ai na musamman suka fara gudanar da bincike a kan lamarin.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya