✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan daba sun tarwatsa zanga-zangar #EndSARS a Kano

Rahotannin daga Kano na cewa wasu gungun matasa dauke da makamai sun auka wa masu zanga-zangar #EndSARS a unguwar Nomansland da ke yankin Sabon Gari.…

Rahotannin daga Kano na cewa wasu gungun matasa dauke da makamai sun auka wa masu zanga-zangar #EndSARS a unguwar Nomansland da ke yankin Sabon Gari.

A ranar Litinin ne dai wasu matasa masu rajin kawo karshen zaluncin ’yan sanda a Jihar Kano suka shiga zanga-zangar #EndSARS daga unguwar ta Nomansland zuwa Sarkin Yaki har suka kawo kan babban titin Airport da ke karamar hukumar Nassarawa.

A safiyar Talata masu zanga-zangar sun sake fitowa kan babban titin Aiport domin ci gaba da zanga-zangar a ranar ta biyu.

Sai dai an yi rashin sa’a inda wasu matasa dauke da makamai suka farmake su tare da tarwatsa su.

Daya daga cikin masu zanga-zangar mai suna Binta Ibrahim, ta shaida wa wakilinmu cewa suna tsaka da gudanar da tattakin ne kawai sai suka ji an hau su da duka da sare-sare.

“Yau da misalin karfe bakwai na safe bayan mun fito domin ci gaba da zanga-zangar ne sai ga motocin ’yan sanda da yawa wai gwamna yana da bukatar ganinmu domin tattaunawa da mu.

“Jagororin tafiyar tamu suka ce babu inda zamu je kuma sai mun ci gaba da zanga-zangar, daga bisani ’yan sandan suka yi tafiyarsu suka kyale mu.

Ta kara da cewa ba su jima da hawa kan titin Airport ba sai gungun matasa su kai musu hari tare da tarwatsa su.

“Yanzu haka muna daidai ofishin makarantar daukan horo ta Immigration inda muka buya a gidan wani mutum”, cewar Binta.

Yanzu haka dai masu zanga-zangar sun tsere domin tsira da lafiyarsa daga hannun wadancan gungun matasan.