✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan fantekan garin Mpape Abuja sun koka a kan filin kasuwa

‘Yan Kasuwar Fanteka da ke gudanar da harkokinsu a garin Mpape da ke Babbar Birnin Tarayya Abuja sun bukaci Karamar Hukumar Bwari Abuja da ta…

‘Yan Kasuwar Fanteka da ke gudanar da harkokinsu a garin Mpape da ke Babbar Birnin Tarayya Abuja sun bukaci Karamar Hukumar Bwari Abuja da ta sama masu fili don gudanar da harkokinsu na kasuwanci a garin cikin tsanaki.

Jagororin kungiyar da ya hada da Shugabanta Alhaji Musa Abdullahi da Sakatare Malam Kazim Aliyu Muhammad da kuma jami’in yada labarai Malam Musa Abdullahi ne suka bayyana bukatar a yayin zantawa da Aminiya.

Kungiyar ta ce ta shafe shekara 20 a matsuguninta na yanzu da ke layin Koroshin a Mpape a matsayin ’yan haya sai gashi a yanzu, “wasu ’yan asalin Abuja da muke biyansu kudin hayan filin sun bukaci da mu tashi don gina rukunin shaguna a wajen. Mun nemi da su sayar mana da filin kamar yadda suka sayarwa wasu daidaikunmu, amma ba su amince ba.

“Sai dai daga baya mun samu labarin cewa wajen na hukuma ne da ba a bukatar a yi gini sai dai zaman wucin gadi kawai, kasancewar akwai babban layin wutar lantarki da ya ratsa ta wajen, kuma a yanzu za a bukaci filin don aikin shimfida babban titi da za a yi zuwa rukunin gidaje da ake ginawa a kauyen Shere ya kuma wuce zuwa garin Bwari.

“To daga nan ne muka daina biyan dan abin da muke ba su, sai dai za a tayar da mu daga wajen a ko wane lokaci daga yanzu, wannan shi ya sa muke kira ga gwamnatin da ta taimaka mana da wani fili don gudanar da harkokinmu na kasuwanci,” inji shugaban.

Alhaji Musa Abdullahi ya kara da cewa kungiyar wadda ta samu nasarar rajista da hukumar yi wa kamfanoni rajista ta kasa wato CAC, sun kafa sabbin dokoki ga mambobin kungiyar da ya ce adadinsu ya kai dubu 5 inda za a rika cin tarar duk wani mamba ko dakatar da shi, idan ya keta dokar.

Laifuffukan kamar yadda kundinsu da suka gabatar ga Aminiya ya zayyana, sun hada da laifin sayan kayan sata da aikata lalata ko fyade ko luwadi, akwai kuma na cin zarafin abokin sana’a, da dai sauransu. Haka nan ya ce a sakamakon rashin banbance tsakanin ’yan-bola da kuma mambobinsu da wasu jama’an gari ke yi da hakan ke jawo masu bacin suna, ya ce kungiyar ta kafawa ’yan bolan dokar hana fita tsintar kaya gabanin karfe 7 na safe sannan kuma da dakatar da aikinsu idan karfe 5 ta yamma ta yi, da ya ce ’yan bolan sun amince.