Search
Subscribe
’Yan fashi sun bindige Sufeton ’yan sanda a Kalaba

Sufeto Janar Ibrahim Kpotun Idris

’Yan fashi sun bindige Sufeton ’yan sanda a Kalaba

Wadansu da ake zargin ’yan fashi da makami ne sun harbe wani dan sanda mai mukamin Sufeto, yayin da yake hanyarsa ta komawa gida bayan ya taso daga aiki.

Jami’in, wanda bai san cewa barayi suna fashi da makami a layin ba, ya hadu da bala’in ne a Layin Otop Abasi da ke Karamar Hukumar Birnin Kalaba a Jihar Kuros Riba.

Yadda aka yi dan sandan ya gamu da ajalinsa, kamar yadda Aminiya ta samu labari, shi ne Sufeto Ebiri Ogban da ke aiki a sashen kula da masu aikata miyagun laifuffuka na Hukumar ’Yan sandan Kuros Riba, shi ne ta samu kiran daukin gaugawa zuwa Layin Otop Abasi, cewa akwai ’yan fashi suna cin karensu babu babbaka, inda ’yan sanda suka yi wa musu kofar rago, domin su kama su. Sai kuma Sufeto Ogban ya biyo ta hanyar, bayan ya taso daga aiki, inda  barayin suka harbe shi, suna tsammanin yana cikin ’yan sandan da ke bin su domin kama su.

Wata wadda abin ya rutsa da ita kuma ta sha da kyar, mai suna Goodnews Etim Efanga ta ce, “Muna zaune a bakin shagunanmu ’yan fashin suka dirar mana. Can sai ga motar ’yan sanda ta biyo layin, kuma sai ga wannan dan sanda cikin kayan aiki. Sai suka yi zaton yana cikin masu bin su ne, nan take suka harbe shi, ya rasu.”

Wakilnmu ya tuntubi Kakakin ’Yan sandan Kuros Riba, Irene Ugbo game da lamarin, wacce ta tabbatar da faruwar hakan. Sai dai ta ce har zuwa lokacin ba su kama kowa ba amma suna yin bincike.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin