Da Dumi Dumi

‘Yan fashi sun kai hari a kasuwar IBB Suleja

Wani gungun ‘yan fashi da su ka kai hari a kasuwar IBB da ke garin Suleja a yammacin jiya Litinin, sun harbi mutum guda daga nan suke tsere daga wajen.

Wasu da ‘yan kasuwar da suka zanta da Aminiya a safiyar yau Talata sun bayyana cewa ‘yan fashin bayan isowarsu wajen da misalin karfe 7 saura a yammacin na jiya, kai tsaye sun zarce zuwa wani shagon sayar da waya da ke rukunin shaguna na Murada, daura da daya daga cikin mashigar kasuwar.

“Sun ajiye motarsu ta Suleja club da ke kusa da Kasuwar, sannan koda suka shiga shagon ba wanda ya san abin da ke faruwa kasancewar sun aiwatar da komi ne a cikin sirri, in ji majiyar.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya