Da Dumi Dumi

’Yan fashi sun kashe matukin Keke NAPEP a Kaduna

Wasu da ake zargin ‘yan fashi ne sun kashe wani matukin Keke NAPEP ‎a kusa da Unguwar Kamazou akan titin Ibrahim Yakowa da ke cikin Kaduna.

A cewar rundunar ‘yan Sandan Jihar wannan kusan gilla ne saboda la’akari da raunuka da ke aka yi wa mamacin mai Suna Benedict Garba mai shekaru 45 mazaunin unguwar Maraban Rido.

Kakakin Rundunar ‘yan Sandan Kaduna DSP Yakubu Sabo, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammancin yau Litinin din nan ga manema labarai.

Ya kuma bayyana cewa, sun samu labarin aukuwar lamarin ne daga bakin jami’in ‘Yan Sandan Sabon Tasha watau DPO cewa, an tsince gawar mamacin ne ranar 9 ga watan Satumba 2019 da misalin 9 na dare.

‎”Hakan yasa aka tura da jami’ai wajen da aka tsinci gawar kuma ga dukkan alamu kusan gilla ne saboda irin raunuka da ya samu a kai. Wannan yasa Kwamishinan ‘yan Sandan Jihar Ali Janga, ya bada umurnin a gudanar da bincike domin sanin wadanda suka aikata wannan lamari.” In ji shi.

ADVERTISEMENT

‎Ya kuma ce, an dauki hotan gawar kafin a kai gawar zuwa wajen ajiye gawa a asibitin Sabo.

Share