✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan fashi sun kashe wani mai otel a Legas

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta tabbatar da mutuwar Mista Olanrewaju Subair mai hotel din da ake kira 04 Hotel da ke unguwar Ajah yayin…

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta tabbatar da mutuwar Mista Olanrewaju Subair mai hotel din da ake kira 04 Hotel da ke unguwar Ajah yayin da wasu gungun ’yan fashi da makami suka kai masa hari a cikin hotel din nasa.
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar Ngozi Braide ta bayyana cewa lamarin ya auku ne a ranar Lahadi lokacin da ’yan fashin suka kai harin ramuwar gayya a hotel din bayan da ’yan sanda suka kama wani shugaban gungun ’yan fashi a otel din a kwanakin baya.
Ta ce ’yan fashin sun gaya wa ma’aikatan otel din cewa sun zo ramuwar gayya ne saboda kama shugabansu da ’yan sanda suka yi. A lokacin an ci sa’a daya daga cikin ma’aikatan otel din ya kira ’yan sanda ta wayar salula, amma ’yan fashin na ganin ’yan sandan sai suka bude wuta inda suka kashe mai otel din suka raunata ma’aikatansa da dama. Amma ’yan sanda sun harbe wani cikin ’yan fashin kuma sun dauki matakan kame sauran da suka gudu.
Wani ganau kan lamarin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan fashin sun kashe budurwar mai otel din tare da mutum biyu kuma mutum biyu sun sami munanan raunuka, saboda goborar da ta tashi a lokacion da ’yan fashin ke musayar wuta da ’yan sanda.
Tuni ’yan sandan kwantar da tarzoma dauke da manyan makamai suka killace otel din don hana mutane da manema labarai shiga ciki.
Daraktan hukumar kashe gobara na jihar, Razak Fadipe ya tabbatar da mutuwar mutum biyu, sakamakon kunar da suka samu a gobarar.