✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan fashi sun kashe ’yan acaba biyu a Kaduna

A ranar Litinin da ta wuce ne wadansu da ake  zargin ’yan fashi ne suka kashe masu sana’ar acaba biyu a gidan sayar da mai…

A ranar Litinin da ta wuce ne wadansu da ake  zargin ’yan fashi ne suka kashe masu sana’ar acaba biyu a gidan sayar da mai na Usmaniyya da ke Kaduna.

Lamarin wanda ya faru da misalin karfe 3:45 na dare ya yi matukar  tayar da hankalin jama’ar yankin.

Aminiya ta samu labarin cewa mamatan biyu sun fito ne daga yankin Karaye da ke Jihar Kano kuma suna kwana ne a wurin dan uwansu da ke aiki a gidan man aduk lokacin da suka je Kaduna don gudanar da sana’arsu ta acaba.

Wani da lamarin ya auku a idonsa mai suna Rayyanu Dawakin Tofa ya ce ’yan fashin wadanda bai san yawansu ba sun karbe wayoyi da kudaden da ke hannunsu kafin su bukaci su kwanta a kasa.

Ya shaida wa Aminiya cewa daya daga cikin ’yan fashin bayan ya doke shi a fuska sai ya bukaci ya kwanta a kasa. “Bayan sun shigo suna rike da bindigogi sai suka ce in ba su wayata, sai na ba su har kudin da ke aljihuna na mika musu sannan suka buge ni da kafa a fuska suka ce in kwanta. Bayan na kwanta sai suka shiga dakin da mamatan ke kwance suka tashe su suka bukaci kowa ya kwanta, sai daya daga cikinmu ya fita a guje yana ihu daga nan ne suka bi shi suka sare shi a kai. Dayan kuma da ya nemi ya gudu sai suka harbe shi a kirji. Nan take suka rasu,” inji shi.

Aminiya ta samu labarin cewa daya daga cikin wadanda aka kashe kwana shida ke nan da dawowarsa daga garinsu bayan ya kai ziyara.

Kuma bayanai sun ce barayin sun tafi da babur din daya daga cikin wadanda suka kashe.

Da yake karin bayani kan lamarin, mai gidan nai na Usmaniyya, Alhaji Abubakar Usman Sharif ya ce ya samu labarin abin da ya faru a gidan mansa ne bayan Sallar Asuba.

Ya ce nan take suka wuce wurin inda ya tarar da daya daga cikin wadanda aka kashe kwance a kusa da famfon da ake sayar da mai an sare shi a kai, yayin da dayan kuma yake kwance a gefe shi kuma an harbe shi a kirji.

“Tabbas na je wurin na gan su a kwance duk a mace, daga nan sai muka sanar da ’yan uwansu, sai dai  ’yan uwan sun bukaci mu yi jana’izarsu a nan saboda a nan aka kashe su,” inji shi.

Ya ce sun sanar da jami’an tsaro halin da ake ciki kafin a yi wa mamatan sutura an kuma binne su ne a makabartar Layin Bashama a Tudun Wada Kaduna.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna Yakubu Sabo ya  tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce tuni rundunar ta soma bincike domin gano wadanda ke da hannu a kisan.

Ya ce ba a sanar da ’yan sanda lokacin da lamarin ke aukuwa ba, sai da gari ya waye sannan aka kai musu rahoto.

“Mun samu labarin  mutum biyu sun rasu a lokacin da wadanda ake zargin ’yan fashi ne suka kai musu hari inda suka sari daya a kai, daya kuma suka harbe shi a kirji. Wadanda suka kai musu harin muna zargin ’yan fashi ne domin sun tafi da babur daya. Mun fara bincike kan lamarin da nufin gano wadanda suka aikata laifin,” inji shi.