Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

’Yan fashi sun kashe ’Yan acaba biyu a Kaduna

Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun kashe wasu mutum biyu masu sana’ar acaba a safiyar yau Litinin a gidan mai na Usmaniyya filling station  da ke hanyar Nnamdi Azikwe a cikin garin Kaduna.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:45 na asubahin yau lokacin da ’yan fashi suka shiga gidan man, sun kwace wayoyin ‘yan acaban da kudadensu kafin su kashe su.

ADVERTISEMENT

Daya daga cikin wanda ya tsallake rijiya da baya daga hannun ‘yan fashin Rayyanu Yahaya Dawakin Tofa, ya ce ‘yan fashin sun shiga gidan man ne da bindigogi da wukake kuma sun kwace duk wayoyin salula da kudaden masu kwana a gidan man.

ADVERTISEMENT