✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan fashi sun kashe ’yan sanda 5 a ayarin Mataimakin Gwamnan Nasarawa

‘Yan sanda biyar ne aka kashe  lokacin da ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi da makami ne  suka far ayarin Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa,…

‘Yan sanda biyar ne aka kashe  lokacin da ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi da makami ne  suka far ayarin Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa, Dokta Emmanuel Akabe a kusa da garin Akwanga.

An kai wa Mataimakin Gwamnan harin ne a wani kwazazzabo da ya yi kaurin suna da ake kira “Many habe gone” wato “Da yawa sun rasu,” a hanyar da ke tsakanin duwatsu a Karamar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa.

Wata majiya daga ofishin Mataimakin Gwamnan ta shaida wa Aminiya cewa Mataimakin Gwamnan ya fito daga Lafiya zuwa Abuja domin halartar wani taro, kuma harin ya auku ne da misalin karfe 7 na yamma.

Wani ganau ya ce barayi ne suka tare hanyar suna fashi da makami, sai Mataimakin Gwamnan da ayarinsa suka karaso wurin, inda nan take ’yan sandan da suke tare da shi suka fara musayar wuta da barayin, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar ’yan sandan.

Wata majiya ta kara da cewa duk da cewa Mataimakin Gwamnan bai ji rauni ba, abin ya firgita shi sosai.

Tuni dai aka kai gawarwakin ’yan sandan zuwa Asibitin Kwararru na Dalhatu Araf da ke Lafiya.