✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan fim mu hada kanmu – dan Soja

Fitaccen mai samar da abinci a wurin daukar fim dan Soja ya bukaci ‘yan fim su zama tsintsiya madauri daya don tunkarar duk wani abu…

Dan sojaFitaccen mai samar da abinci a wurin daukar fim dan Soja ya bukaci ‘yan fim su zama tsintsiya madauri daya don tunkarar duk wani abu da ya tunkare su.
Ya ce: “Bai kamata a ci gaba da zama kara zube ba, ya kamata mu rika magana da yawu daya, a samu wata kungiya mai karfi da kowane dan fim zai kasance a karkarshinta, yin hakan zai sanya a samu alkibla daya.”
Ya ce, a halin da ake ciki kowa da inda yake biyawa kamar almajiran tsangaya, hakan ya nakasa harkar, da akwai tsayayyen shugabanci da harkar ta wuce inda take a yanzu.
A karshe ya nemi ’yan fim su hada kai da ’yan jarida don isar da sakonninsu wurin masoyansu, “yan jarida abokanmu ne, kuma idan muka hada kai da su, masana’antarmu za ta tumbatsa.”