✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan gudun hijirar Borno 20 sun rasu wajen rabon tallafi a Nijar

Rahotanni sun ce kimanin mutum 20 wadanda akasarin su mata ne da yara suka rasu sakamakon cinkoson da aka samu wajen rabon tallafin kaya da…

Rahotanni sun ce kimanin mutum 20 wadanda akasarin su mata ne da yara suka rasu sakamakon cinkoson da aka samu wajen rabon tallafin kaya da kudi da Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai wa ’yan gudun hijirar da ke garin Diffa a Jamhuriyyar Nijar, kamar yadda Aminiya ta samu labari.

Majiyarmu ta ce kuma mutum 12 samu rauni a yayin rabon “Muna da tabbacin mutum 20 sun rasa ransu, yayin da 12 suka samu rauni,” wani jami’in lafiya ya tabbatar wa Aminiya.

Sama da mutum dubu 30 ne ke gudun hijira a garin Diffa na Jamhuriyar Nijar ne, sakamakon tarwatsa su da ’yan Boko Haram suka yi daga garuruwansu suka samu tallafin kayayyakin da  Gwamna Zulum ya kai da suka hada da kayan abinci da sutura da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum.

A ranar Lahadin da ta gabata ce Gwamna Zulum ya kai ziyarar, irinta ta farko ga ’yan gudun hijirar, kafin ya isa garin Diffa, sai da ya yada zango a garin Malumfatori, Hedikwatar Karamar Hukumar Abadam, garin da a da matattarar Boko Haram ne.

Farfesa Zulum ya gana da manyan jami’an gwamnatin Nijar a garin na Diffa kan yadda za a inganta rayuwar ’yan gudun hijirar, kuma yanzu haka akwai ’yan gudun hijira dubu 120 a garin da suka fito daga kananan hukumomin Abadam da Mobbar da Kukawa da Guzamala da ke Arewacin Jihar Borno.

Baya ga buhunan shinkafa da masara da man girki, an raba wa ’yan gudun hijirar zannuwa da wasu kudi.

Gwamna Zulum ya gode wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce dubban buhuhunan shinkafa da aka raba Gwamnati Tarayya ce ta bayar da su ta hannun Hukumar Kwastam.