Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

’Yan gudun hijirar Sakkwato na son barin sansani amma mahara na kara ta’asa 

‘Yan gudun hijira a garin Gandi a Qaramar Hukumar Ravah, Jihar Sakkwato Hotuna daga Nasiru Bello
‘Yan gudun hijira a garin Gandi a Qaramar Hukumar Ravah, Jihar Sakkwato Hotuna daga Nasiru Bello

Watanni 11 ke nan da ’yan gudun hijira sama da dubu 10, manya da yara maza da mata daga kauyuka 10 da ke kusa da garin Gandi a Karamar Hukumar Rabah a Jihar Sakkwato suke zaune a sansani, bayan an kashe sama da mutum 100 a hare-haren da ’yan bindiga suka kai kauyukan.

A wadannan hare-hare, an yi jana’izar mutum 38 a garin Tabanni a lokaci daya, inda 37 daga cikinsu maza ne magidanta, daya kuma mace. Sannan an samu yara 37 da suka fada tafkin garin suka rasu. An kone wadansu mutanen da wuta, wadansu kuma suka shiga daji sun rasu.

ADVERTISEMENT

A kauyukan Warwarna da Dutse da Kursa, an kashe mutum 25 har da hakiminsu. A Gidan Kari kuma mata 22 suka rasa ransu.

Sai dai kuma ’yan gudun hijira sun koka kan ci gaba da zama a sansanin gudun hijira duk da cewa suna samu abinci da sutura. Shugaban ’yan gudun hijirar kauyen Tabanni, Malam Muhammad Lawal ya ce Gwamna ne ubansu, kuma y ce tunda suka shigo garin Tabanni, Yarin Gandi ya mika su ga hannun Gwamna, ba yi su yunwar abinci da sutura ba ko rana daya ba, ba su samu matsala ba har a wurin ba su magani.

ADVERTISEMENT

“Yanzu watanmu 11 a cikin garin Gandi, wani magidanci tun lokacin rabonsa da iyalinsa. Kan haka muke bukatar a samar mana wani matsugunni mu bar wannan firamare da muke ciki. Ba za mu koma kauyenmu Tabanni ba, don har yanzu akwai matsala. Muna son Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya samar mana da fili kusa da garin Gandi, a ba mu don killacewa da iyalanmu da kula da karatun ’ya’yanmu mu janye wa yaran Gandi wuri su ci gaba da karatu. A halin da ake ciki karatun yaranmu da nasu ya lalace, a samar mana inda za mu yi noma don talaka ba ya iya ci gaba da zama ba zuwa gona,” inji Lawal.

Jafaru Muhtaru Tabanni, dan shekara 31 ya ce, “Mu ’yan gudun hijira za mu kai 300 a Tabanni kadai. Maharan sun kone mana abinci a rumbunanmu, ko’ina suka gani sai sun cinna masu wuta, abin da ke ciki ya kone; ga kashe mana Hakimi da suka yi Marafan Tabanni da ’ya’yansa bakwai; biyu kawai suka bari da ransu. Ba abin da muka rasa a nan sai dai muna son a samar mana wajen da za mu koma da iyalanmu don samun walwala da sakewa.”

Mamman Yusuf ya ce mutanen da ke zaune a sansanin ba za su wuce na kauye uku ba, sauran kauyukan sun koma mazauninsu. Kan haka matsalolin sansanin suka ragu sosai, amma dai har yanzu akwai karancin wurin ba-haya. A lokacin damina kuma ruwa yana shiga tantinsu ko iska ta dauke shi. Ya ce babu abin da ya fi kamar a samar musu da sabon matsugunni su koma don samun walwala. “A yanzu mutanen da ke cikin sansanin ba su kai 1000 ba,” ya bayyana wa Aminiya.

Sai dai kuma fatar ’yan gudun hijirar ta fara gushewa a farkon makon jiya, bayan da ’yan bindiga suka kara kai sabon hari a wasu garuruwa a jihar.

Sabon harin, wanda ya faru a ranar Asabar din makon jiya, ’yan bindigar sun kashe mutum 47 a kauyuka bakwai da ke kananan hukumomin Isa da Rabah.

Maharan sun fara yi wa kauyen Satiru kawanya ne da misalin karfe biyar na yamma, lokacin da mutanen garin suka fita yin shuka saboda ruwan saman da ya sauka.

“Ta ko’ina cikin kauyen harbin bindiga kake ji. Sun shigo garin a kan babura kamar yadda suka saba, suka kashe mutum 12 nan take, suka raunata mutum 18. Daga nan suka wuce Baiti da Katanga, inda suka kashe mutum 10, duk a yankin Isa,” wata majiya ta shaida wa Aminiya.

Majiyar ta kara da cewa “Akwai wata mata a Satiru da ta fita hayyacinta kan harin da aka kai. Saboda maharan sun kashe mata mahaifi da miji da kanenta, sun jikkata yayanta yana asibiti yana jinya. Ba ta iya yin komai sai kuka kawai. Ta shiga tashin hankali, har suma ta yi. Barayin sun addabi yankin, domin a kwanan baya sun yi garkuwa da Marafan Tozai da dansa, suka nemi a ba su Naira miliyan biyu da rabi, sai ga shi kuma yanzu sun shi wannan ta’asar.”

Shugaban Jam’iyar PDP na Karamar Hukumar Isa, Alhaji Baraya Tunau ya aika gudunmawar shinkafa da dawa ga wadanda lamarin ya sama tare da jajanta musu.

A Karamar Hukumar Rabah, maharan sun kashe mutum 25 a kauyen Rokanni da Malelawa da Kalfu da Gi’ire, a cikin dare ranar Asabar din makon jiya.

Lauwali Muhammad ya ce mutanen sun zo musu kamar yadda suka saba a kan babura, mutum biyu rike da bindiga, daya na tuka babur. “Ba su shiga cikin gidan kowa ba, amma duk wanda suka samu a hanya sai su kashe shi, an tantance mutanen da suka rasu gaba daya, maza 24 da mace daya kuma an yi musu Sallah a garin Gandi. Gwamnati ta yi sansanin ’yan gudun hijira a firamaren garin Kurya. Maharan sun kwashi shanu da awaki da tumaki amma zuwa yanzu wasu shanu 25 sun dawo, inji shi.”

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Sakkwato, Ibrahim Ka’oje ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce an kama mutum hudu da ake zargin suna da alaka da harin. A cikinsu akwai wanda ya sauya kama ya yi shigar mahaukaciya, shi ake zargi da ba da bayani kan shirinsu.

Ka’oje ya kara da cewa za a ci gaba da bincike sai an zakulo sauran maharan.

Gwamna Aminu Tambuwal yana cikin wadanda suka sallaci mamatan, ya kuma yi jaje ga iyalai da iyayen kasar Rabah. Ya tabbatar musu da cewa gwamnatinsa na aiki tukuru don kawar da batagari a jihar.

Shugaban kula da walwalar ’yan gudun hijirar, Malam Muhammad Lawal Maidoki ya ce sun kai kayan agajin gaggawa ga mutanen kuma za su ci gaba da kula da su har yadda yanayi ya bayar. A cewarsa, sun kai musu duk wani abu da suke bukata da gwamnati ta bayar.