✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan Gwangwan sun koka kan yadda masana’antun kasashen waje ke musguna musu

Wadansu masu sana’ar gwangwan a Jihar Legas sun koka kan yadda masana’antun da ke mu’amala da su ke musguna musu ta hanyar karyar da farashin…

Wadansu masu sana’ar gwangwan a Jihar Legas sun koka kan yadda masana’antun da ke mu’amala da su ke musguna musu ta hanyar karyar da farashin kayayyakin da suke saya a wajensu, lamarin da ke janyo wa ’yan gwangwan tafka mummunar asara.

A wata kwarya-kwaryar zanga-zangar lumana da ’yan gwangwan din suka shirya a ranar Litinin a harabar ofishinsu na Legas da ke Gidan Kwali a Ojota, mambobin Kungiyar ’Yan Gwangwan sun sha alwashin shiga yajin aikin Sai-Baba-Ta-Gani muddin masana’antun da ke sayen kayan nasu ba su daidaita farashin ba, inda suka kaddamar yajin aiki na gargadi na kwana uku da ya soma daga ranar Litinin. Sun yi barazanar hana sayar da kayayyaki ga masana’antun a duk fadin kasar nan muddin ba su yi dubi koke-kokensu ba.

Da yake zantawa da manema labarai shugaban Kungiyar ’Yan Gwangwan ta Kasa, Alhaji Kukan Onifade, ya ce, masana’antun da ke sayan kayayyakinsu mallakar ’yan kasar China da Kwarori suna yi musu zagon-kasa domin bayan sun ba su farashin da za su nemo musu kaya, sai su yi taro a tsakaninsu su karyar da farashin. “Wannan harka tamu ta gwangwan tana da rukuni uku; da masu nemo kayan da masu saye da su masana’antun ’yan China da Kwarori da ke sayen kayan a hannun dillalai. Matsalar da muke fuskanta za su ba mu farashi, sai bayan mun sayo kayan a wannan farashi mun tara musu, sai su hada baki su karyar da farashin.

A irin haka ne a makon jiya na yi ido hudu da wani dattijo yana ta kuka a bakin wata masana’anta da ya kai wa kaya bayan sun karyar masa da kayan ya yi asarar Naira dubu 450. Ai ka ga wannan hasara ba karama ba ce. Don haka ba za mu zuba ido mu bari su ci gaba da yi mana lahani ba, wannan abu ya janyo da dama daga cikinmu bashi ya hau kansu. Don haka muka fito mu bayyana wa duniya irin halin da muke ciki kana mu nema wa kanmu mafita domin ba za ta sabu ba, baki suna zuwa kasarmu suna yi mana zagon kasa,” inji shi.

Alhaji Abdullahi Soja, Sarkin ’Yan Gwangwan na jihohin Yamma ya shaida wa Aminiya cewa ilahirin ’yan Kasuwar Gwangwan da ke kasar nan za su yi yajin aiki na illa masha Allahu da zarar sun kammala yajin aikin gargadi na kwana uku, muddin kwaliya ba ta biya kudin sabulu ba, “Zagon kasa da masana’antun ke mana sun sanya da dama daga cikinmu bashi ya hau kansu, domin akasari kudi muke amsa daga bankuna mu sayi kayan, to yaya suke so mu biya bankunan da wannan zagon kasa da suke mana? Muddin ba su sauya ba, za mu dakatar da kai musu kaya a duk fadin kasar nan,” inji shi.

Shugabar Mata ta Kungiyar, Hajiya Taibat Alaka, ta shaida wa Aminiya cewa, kamata ya yi idan masana’antu za su sauya farashi su rika tuntubar mambobin kungiyar sannan sun sanar musu akkala cikin wata uku, domin ’yan kasuwar na tafka asara kuma hakan ba adalci ba ne.

Shugaban Kungiyar ’Yan Gwangwan Reshen Jihar Legas, Kwamared Friday,  ya ce sana’ar gwangwan harka ce mai matukar muhimmanci a kasar nan, lura da gudunmawar da take bayar wa wajen sama wa dimbin mutane ayyukan yi, tare da rage radadin talauci da kuma tsabtace kasa da samar da kayayyakin amfani daban-daban da suka hada da rodin gine-gine da sauransu. Don haka kamata ya yi gwamnati ta shigo lamarin domin ta magance matsalar da suke fama da ita a harkar domin idan gwamnati ta zuba wa kamfanonin kasashen ketare ido suka lalata sana’ar, dubban al’umarta ne za su shiga garari.