✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Kannywood sun lashe kyaututtuka a Landan

A ranar Asabar da ta gabata ce ’yan Kannywood suka lashe manyan kyaututtuka a bikin karrama ’yan fim a birnin Landan. ’Yan wasa irin su Rahama…

A ranar Asabar da ta gabata ce ’yan Kannywood suka lashe manyan kyaututtuka a bikin karrama ’yan fim a birnin Landan.

’Yan wasa irin su Rahama Sadau ta lashe jaruma mafi kwazo a Afirka na shekarar 2019, sai Fati Washa da ta lashe gwarzuwar jaruma ta shekarar 2019 bisa rawar da ta taka a fim din Sadauki.

Haka kuma Ali Nuhu ya lashe kyautar gwarzon darakta na shekarar 2019 da fim dinsa na Kar Ki Manta Da ni, sai kuma Jamilu Yakasai.

Bayan sun karbi kyaututtukan ne, wanda Ali Nuhu bai samu zuwa ba, sai Rahama Sadau da Hadiza Gabon da Fati Washa suka sanya wasu hotuna da suka jawo cece-ku-ce, inda wadansu suke ganin cewa sun yi shiga wadda ta saba wa addini da al’adar Hausawa, ganin cewa sun je Landan din ne a matsayin wakilan Hausawa.

An yi bikin ne a dakin taro na Old Town Hall da ke Broadway, Stratford a Landan, kuma wannan shi ne karo na 23.

Irin yadda aka rika caccakarsu duk da cewa wadansu sun yaba da irin shigar da suka yi ya sa jaruma Hadiza Gabon ta mayar da martani mai zafi ga wani daga cikin masu caccakar, sannan ita ma Rahama Sadau ta mayar da martani, duk da cewa daga baya sun cire martanin da suka yi.

Daga baya Hadiza Gabon ta rubuta wani sakon, inda take bayyana neman gafara ga Allah da kuma ba mutane hakuri bisa martanin da ta mayar da farko, wanda hakan ya burge mutane, ciki har da Ministan Sadarwa,  Dokta Isa Ali Pantami

A sakon nata, cewa ta yi: “Astaghfirul lah kan martanin da na mayar marar kyau kan wata amsar rashin da’a da wani ya ba ni. Na goge sakon kuma na nemi gafarar Allah kan kokarin mayar da martani cikin fushi kan wani kuskuren da aka yi.” Kamar yadda BBC ya ruwaito.

Bayan haka ne Ministan Sadarwa Isa Ali Pantmi ya bayar da amsa a kasan sakon, inda ya ce,”Wannan babban abin a yaba ne a nemi gafarar Allah bayan yin wani kuskure. Allah Madaukakin Sarki Ya yafe mana Ya kuma yi mana jagora tare da kare mu a gaba,” inji shi kamar yadda BBC ya ruwaito.