✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kasuwa na da takaicin jami’an kwastam

Dokta Abdullahi Inde (shugaban kwastam na Najeriya), yana daga cikin wadanda muke kyautata wa zato daga cikin jami’an tsaron wannan kasa. Kuma har ga Allah,…

Dokta Abdullahi Inde (shugaban kwastam na Najeriya), yana daga cikin wadanda muke kyautata wa zato daga cikin jami’an tsaron wannan kasa. Kuma har ga Allah, yana iya kokarinsa domin ceto wannan al’umma tamu kamar yadda muke hange. To sai dai kowane mutum dan tara ne bai cika goma ba, wannan ce ta haifar da hatta jami’an kwastam da ke karkashinsa suke tsoratar da mutane yadda suke so musamman akan iyakokin kasa-da-kasa, da kuma manyan hanyoyin da suke tsayawa da sunan bincike ko in ce tabbatar da aikinsu. Ashe matsalar ba ta tsaya akan ‘yan sanda ba su kadai.
Binciken da na yi akan wannan bangare, ya tabbatar da cewa jami’an kwastam suna da hannu dumu-dumu a cikin matsin rayuwa da ake fama da shi, da kuma kara dagule harkar kasuwancinmu. Duk wannan tana faruwa ne, saboda an daurewa wasu tsirarun mutane gindi, domin su kara arzitta kawunansu tare da habaka kasuwancinsu. Wadannan mutane ba su wuce ka lissafe su da dan yatsa ba, amma akan a faranta musu rai, sai ake sanya mutane sama da miliyan 100 kunci da kuma rashin walwala. Ake wulakanta ’yan kasuwa masu karamin karfi, ake takura wa masu matsakaicin karfi, ta hanyar danne musu hakkinsu, wasu lokuta kuma a nemi cin hanci daga gare su kafin su samu damar shigowa da kayan masarufi a cikin wannan kasa.
Yanzu dai kusan kowa ya gane inda na dosa! Sauran da ba su gane ba, su biyo ni mu je.
Duk wani dan kasuwa da ke fita daga Najeriya ya shiga jamhuriyar Nijar, domin ya sayo wasu kayan da zai dawo ya sayar a Najeriya, to kada ka ware kowaye ma, idan ka tambaye shi, zai tabbatar maka da cewa yana cike da bakin ciki da jin haushin jami’an kwastam a ransa. Wannan kuma ba don wai suna tsare aikinsu ba, A’a! Sai dai don tsabar cin hancin da ake karba a hannuwan ‘yan kasuwar da kuma muzgunawa ta babu gaira babu dalili.
Ina ma laifin ace muzgunawar ce kawai! Sai muce ba laifi ba ne. Ya zama dole jami’an kwastam din su tsawaita bincike ga duk kayan da za a shigo da su a Najeriya, koda kuwa zai zama takurawa ga y’an kasuwar, idan dai aka yi la’akari da kalubalen tsaro da muke fuskanta. To sai ya zamo cewa ba wai su binciki kayan da za a shigo da su ba ne gabansu, abinda ke gabansu kawai shi ne, kudin gyaran hanya (cin hanci) da za a ba su.
Ya kai maigirma Dokta Abdullahi Inde, akwai bukatar ka zare damtse domin tabbatar da kirarin da ake yi muku na Katsinawan Dikko, da kunya an ka sanku ba tsoro ba. Al’amarin jami’an da ke karkashinka fa ya bace. Su suke takura ‘yan kasuwa matukar takurawa, sai su kuma ‘yan kasuwa su takura muna ta hanyar tsadatar da ababen sayarwa, don su samu fitowar kudaden da ake amshewa a hannuwansu akan hanya.
Yawaitar makamai a hannun farar hula ma ba zai rasa nasaba da wannan al’amari ba, saboda akwai wadanda ko mai za su shigo da shi a Najeriya ba sai an binciki motarsu ba. Dalili kuma wai sun saye hanya. Har ila yau, ana amfani da wannan damar domin shigowa da miyagun kwayoyi. Amma tare da haka, buhu daya tak na gumi ba ka isa ka shigo da shi a Najeriya ba koda ka bayar da cin hanci kuwa.
Ba abin mamaki ba ne, saboda shi gumi yana daga cikin nau’in abinci, kuma akwai wasu shafaffu da mai ’yan gatar gwamnati, wadanda ake so kada kowa ya shigo da komai a Najeriya na abinci idan ba su ba. Wannan hakika zalumci ne mai girma da ke bukatar a kawo karshensa. Saboda ya haifar da tsadar abinci da karancinsa,  abinda ke saka mutane cikin kunci da tsadar rayuwa.
Sarkin yawa ya fi sarkin karfi, in ji Bahaushe. Na san lamarin ya fi karfin Dokta Inde shi kadai. Saboda matsalar siyasar ubangida da muke fama da ita. Amma idan muka hadu dukanmu muka kawar da duk wani azzalumin shugaban da ke daure wa wani dan kasuwa gindi, a zabe mai zuwa, muna sa ran komai ya zama daidai.
A gaskiya, jami’an kwastam su ma ba gwamnati kadai suke yi wa aiki ba, sukan taimaka wa wasu tsirarun mutane su cika mummunan burinsu, a daidai lokacin da cikar burin wadancan din yake zama takurawa ga mafi yawanci. Wadancan shafaffun dai an sansu, kuma an san yaransu. Maganar a fili take.
Daga sama har kasa akwai gyara, Abdullahi Inde ka fi ni sanin haka. Don Allah a gyara. Ba na fatar Allah Ya tsareka wurin hisabi akan hakkin al’umma. Kai mutum ne mai son kamanta gaskiya, kuma ga kishin kasa da addini a tare da kai. Tabbas jami’anka tsoro suke bai wa al’umma ba tsaro ba.
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah.

Nasir Abbas Babi
08033186727/08095653401