✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan kasuwa su rika bayar da gudunmawa ga harkar wasanni – Ibrahim Galadima

Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Galadima ya ce harkar wasanni ba kawai ta gwamnati ba ce, harka ce da ’yan kasuwa za…

Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Galadima ya ce harkar wasanni ba kawai ta gwamnati ba ce, harka ce da ’yan kasuwa za su iya zuba jari a ciki har  ma su kai ga samun gwaggwabar riba.

Alhaji Ibrahim Galadima ya bayyana haka ne a lokacin taron kaddamar da kwamitin shirya babban taron masu ruwa-da-tsaki a harkar wasanni a jihar.

Alhaji Ibrahim Galadima ya kara da cewa ana samun kalubale a sha’anin  tafiyar da harkar wasanni a jihar hakan ya sa suka kira masu ruwa-da-tsaki a harkar don lalubo hanyoyin da za a tallafa wa harkar wasanni da sababbin shirye-shirye da tsare-tsare  da za su bunkasa harkar wasanni a jihar.

Da yake ba ’yan kasuwar tabbaci, Alhaji Galadima ya ce Gwamnatin Jihar Kano tana iyakacin kokarinta wajen tallafa wa harkar wasanni baya ga hazikan ’yan wasa da Allah Ya albarkaci jihar da su. Don haka akwai tabbacin kwalliya za ta biya kudin sabulu. “Muna ba ’yan kasuwa tabbacin cewa hukumarmu na gudanar da komai a bayyane don haka suna da tabbacin aminci na dukiyarsu, musamman idan aka yi la’akari da cewa gwamnatin jihar tana da sha’awa wajen bunkasa harkar wasanni. Muna kiran masu hannu-da-shuni su shigo cikin harkar don tallafa wa matasan jihar,” inji shi.

Shugaban Kwamitin Wasannin Alhaji Tajudden Dantata ya bayyana muhimmancin wasanni ga rayuwar dan Adam inda ya ce wasa abu ne da yake samar wa matasa aikin yi baya ga dauke hankulansu daga aikata ayyukan assha.

Ya bayar da tabbacin cewa a karshen taron kwamitin nasa zai fito da hanyoyi da za su amfani harkar wasanni gaba daya.