✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kasuwa sun karrama tsohon Daraktan Kasuwar Sakkwato

Kungiyar ’Yan Kasuwar Babbar Kasuwar Sakkwato ta karrama tsohon Babban Daraktan da ya jagoranci kasuwar na tsawon shekara biyu, kuma Babban Sakataren a Ma’aikatar Kananan…

Kungiyar ’Yan Kasuwar Babbar Kasuwar Sakkwato ta karrama tsohon Babban Daraktan da ya jagoranci kasuwar na tsawon shekara biyu, kuma Babban Sakataren a Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta Jihar Alhaji Rufa’i Ibrahim.

Shugaban ’yan kasuwar Alhaji Abubakar Altine ne ya jagorancin tawagar shugabannin kasuwar a wurin karramawar, inda ya ce ba a taba samun darakta irinsa ba, wanda ya dauki kowa daya ba ya danne hakkin kowa a lokacin mulkinsa.

“Ba a yi shugaban da ya gyara Kasuwar Sakkwato irinsa ba, ya gyara mana fitilun kasuwa bayan tsawon lokaci suna mace, ya shawo kan matsalar tsaro wanda a baya sai a fasa shago sama da 20. Saboda jajircewar da ya yi wajen kawo mana ci gaba a cikin kasuwarmu muka ga ya da ce mu karrama shi,” inji Altine. Ya ce tunda aka gina kasuwar ba su kafa kungiya ba sai a shekarar 2010, domin hada kan ’yan kasuwar da ci gabansu.

A jawaban shugabannin kungiyoyin Ibo da Yarbawa na kasuwar sun tabbatar da irin ci gaban da tsohon daraktan ya kawo musu a kasuwar. “Shekarata 35 a cikin kasuwar Sakkwato ban taba hulda da shugaba kamar wanda muka karrama ba, ba na da-na-sanin zama a Sakkwato da shiga cikin wadanda za su karrama wannan mutum,”  inji Miftahu Musa Shugaban Yarbawan Kasuwar Sakkwato.

“Na shafe shekara 18 ina kasuwanci a nan, Jihar Sakkwato ta zama gida gare ni tunda nake kasuwanci ban ga shugaba kamar wannan ba, shi ne ya sanya na ba da goyon baya a karrama shi domin masu zuwa su yi koyi da halinsa na sakin fuska da son kawo gyara,” inji Shugaban Ibo na kasuwar.

A jawabin godiya Alhaji Rufa’i Ibrahim, ya ce, “Lokacin da aka kai ni kasuwar an kira ni a waya sau 180 ana ce min an kai ni wurin matsala, amma har na bar wurin tsawon shekara biyu ban ga wata matsala ba daga ’yan kasuwar, aiki aka kawo ni kuma na yi aikina cikin kwanciyar hankali.”

Ya yi kira ga ’yan kasuwar su dore da halinsu na hadin kai kuma duk lokacin da suke da wata shawara ko neman gudunmawa kofarsa a bude take ga kungiyar ko ya bar kasuwa yana tare da su.