Da Dumi Dumi

’Yan Kasuwar Alabar Rago sun koka kan yunkurin tashinsu

Shugabar Karamar Hukumar Iba, Misis Ramat Adebayo lokacin taron
Shugabar Karamar Hukumar Iba, Misis Ramat Adebayo lokacin taron

‘Yan Kasuwar Alabar Rago da ke  Legas, sun koka da abin da suka ce yunkuri ne na korarsu daga kasuwar da suka kafa sama da shekara 40,  inda suka  ce Shugabar Karamar Hukumar yankin na kokorin yi musu rufa-rufa da sunan mayar da kasuwar ta zamani.

A wani zama da Shugabar Karamar Hukumar Iba, ta yi da shugabannin kasuwar da shugabannin masarautun gargajiyar yankin da kuma dan kwangilar da za a bai wa aikin sabunta kasuwar Shugabar Misis Ramat Rachel Adebayo Oseni, ta bayyana dalilin yunkurin mayar da kasuwar ta zamani kasancewarta a birnin Legas. Ta ce kasuwar ta kasance a cikin kazanta da rashin gyara, don haka ya zama dole a rushe ta a sake gina ta yadda za ta yi daidai da zamani.

A zantawar da Aminiya ta yi da Shugabar Karamar hukumar Iba, bayan kammala taron wanda ya gudana a ranar Litinin da ta gabata ta ce, za a sauya wa kasuwar fasali ne domin tsabtace ta daga kazanta da kare lafiyar masu saye da sayarwa a kasuwar da kyautata yanayin tsaro domin a cewarta kasuwar na zama mafaka ga batagari.

A bangaren shugabannin kasuwar wacce akasarin masu  hada-hada a cikinta ’yan Arewa ne sun nuna kin amincewarsu da yunkuri Shugabar Karamar Hukumar ke yi na sake ginin kasuwar inda suka ce ba su yarda a bai wa wani dan kwangila daga waje ba, a ce shi ne zai zo ya tashe su, ya sake ginin kasuwar sannan daga baya ya sayar musu rumfunan da tsada lamarin da zai yi sanadiyar kwace kasuwar daga hannu ’yan Arewa da suka raya wajen shekaru da dama da suka shude.

Shugaban Kasuwar Alabar Rago Alhaji Malami Ibrahim, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan kasuwar ba adawa suke da gyara ko sabunta kasuwar ba, sai dai tsoron da suke yi kada a yi masu sakiyar da babu ruwa. Saboda sun tabbatar shigo-shigo ba zurfi ake so a yi musu a kore su da karfin tsiya. “Koma  mene ne babu wanda zai sauya wa kasuwar suna domin in ka lura wannan kasuwa ce ta ’yan Arewa kuma sana’ar awaki da tumaki ne kashin bayan kasuwar, don haka yaya za a kawo mana dan kwangilar da bai san al’adunmu da yadda muke kasuwancinmu a ce shi zai sake gina mana kasuwa? Mene ne gamin sana’ar rago ko saniya da ginin bene ko masu kashe gobara? Wannan tsari da dan kwangilar ya zo da shi ba abu ne da za mu aminta ba, idan gyara suke so, sai su ba mu iko mu gyara kasuwar mu da kanmu. Duk tsawon shekarun da muke a kasuwar mu ke gyaranta mu muka ginata gwamnati ba ta taba tallafa mana wajen gyara ba, koda da bulo daya ne duk da makudan kudin harajin da muke bai wa gwamnatin a kowane mataki,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Sarkin Kasuwar Alabar Rago Alhaji Umaru Nagwaggwo, ya shaida wa Aminiya cewa, abin da ya kamata Shugabar Karamar hukumar ta yi shi ne ta kyale ’yan kasuwar su yi aikin sabunta kasuwar da kansu, domin suna da halin yin haka. Ya ce maganar da Shugabar Karamar Hukumar ke yi cewa, tana kokarin kara yawan haraji ne ba ta taso ba, domin suna yin bakin kokarinsu wajen tara wa gwamnatin haraji.

“Muna da daruruwan shaguna a nan, sannan duk wata kowane shago na bai wa gwamnati Naira dubu hudu sannan duk ranar Allah duk matar da ke sayar da abinci na ba da harajin Naira 200. Kazalika sauran masu karamar sana’a suna biyan nasu harajin, amma duk da haka babu aikin da gwamnati ta taba yi a kasuwar sai yanzu suke yunkurin su karbe kasuwar daga hannunmu. Wannan kasuwa ce da  mu sama da miliyan ke cin abinci a ciki idan suka yi wannan abu jama’a da dama za su shiga wani yanayi. Don haka ina kira su dubi kokenmu, a sake  zama domin a ji ta bakin ’yan kasuwa a bi hanyar da kowa zai amfana,” inji shi.

A lokacin taron dan kwangilar da aka bai wa aikin sabunta kasuwar ya nuna wa ’yan kasuwar da sauran mahalarta taron sabuwar taswirar kasuwar lamarin da ’yan kasuwar suka ce bai yi daidai da tsarin kasuwancin da suke yi a kasuwar ta Alabar Rago ba.

Share