✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kasuwar dabbobi sun koka kan rashin riba a Kuros Riba

Masu sayar da dabbobi da suka kai talla Jihar Kuros Riba sun ce cinikin bana babu riba sai ma faduwa  da suka yi. Data daga…

Masu sayar da dabbobi da suka kai talla Jihar Kuros Riba sun ce cinikin bana babu riba sai ma faduwa  da suka yi.

Data daga cikin ’yan Musbahu Muhammad da ya kai raguna zwuwa Jihar Kuros Riba daga Jihar Jigawa ne ya bayyana wa wakilin Aminiya haka a Kalaba. Ya ce “Ragon da a sari muka sayo shi Naira dubu 40 an sayar da shi Naira dubu  32 zuwa  dubu 33, mun danganta hakan da kukan da mutanen gari suke yi na babu kudi ne ya haddasa haka.”

Ya ce tunaninsu rashin kudin da jama’a ke kokawa ya jawo musu amma “Mu mun san daga Allah ne dole kowane dan kasuwa ya san samu da rashi wata rana ya samu wata rana zai iya rasawa ”.

Musbahu Muhammad ya ce “Akalla raguna 24 daga cikin 140 da  muka sayo domin mu sayar a ci riba mun sayar da su  bisa faduwa.” Sai dai cinikin bara ya sha bamban da bana, saboda “Kamar yadda aka yi kasuwa bara mu bana ba ta zame mana haka ba ,saboda mun ga ta yi kasa a kan bara shi ya sa muka fara tunanin rage yawan dabbobin da muke kawowa talla zuwa Kalaba a badi saboda an ji jiki kasuwar ta bana.”

Ya ce raguna 25 da suka rage ba a saya ba ala-tilas suka karayar da farashinsu suka sayar domin su koma gida a sake shirin kasuwar badi.

Wata matsala da dan kasuwar ya koka da ya ce sun fuskanta ita ce matsalar da suka fuskanta a hanya tun daga Abakaliki a Jihar Ebonyi zuwa nan Kuros Riba a hannun masu karbar kudin jangali da masu kula da wucewar ababen hawa  a da suka karbi kudin jangali Naira dubu goma-goma a kowane shinge kan mota, wasu shingayen kuma Naira dubu hudu ko dubu biyar lokacin da suka shiga Jihar kuros Riba “Wuri daya ma mun biya jangali sau hudu a kowane shingen jami’an tsaro da na masu karbar jangali tun daga Jihar Jigawa zuwa Kudancin kasar nan. Mun kashe kimanin Naira dubu 130 kafin mu isa kasuwar da za mu sauke kaya,” inji shi.

Ya bukaci gwamnati ta duba lamarin wadanda take ajiyewa a kan hanya suna duba ababen hawa domin wadansunsu lamarin nasu sai dai addu’a, saboda tsananta wa ’yan kasuwar da suke yi.