Da Dumi Dumi

’Yan kasuwar Kaduna sun fara addu’o’i domin kada a rusa masu shaguna

Wasu ‘yan kasuwa da ke sana’o’insu a cikin kasuwar barci sun fara addu’o’i na musamman domin kada gwamnatin jihar Kaduna a karkashin mulkin Malam Nasir El-Rufai ta rusa masu shaguna a kokarinta na fadada kasuwannin jihar.

Aminiya ta samu rahoton cewa tun bayan bayyana shirin fadada kasuwannin jihar da Gwamna Nasir El-Rufai ya yi a makonnan yawancin ‘yan kasuwa sun shiga rudani da damuwa wadda ta sa suka fara yin addu’o’i na musamman domin ganin shirin bai tabbata ba.

Wasu daga cikin ‘yan kasuwar Barci da Aminiya ta zanta da su sun nuna matukar damuwarsu akan shirin na gwamnan domin a cewarsu bai kamata a rusa kasuwar ba alhalin ba a basu wani wurin da za su koma da sana’arsu ba.‎

Sani Muhammad, ‎wanda tela ne a kasuwar Barci ya ce, hakika ‘yan kasuwa na cikin damuwa tun bayan jin bayanan Gwamna Nasir El-Rufai a radiyo inda ya bayyana kudirinsa na fadada Kasuwar Barci da sauran wasu kasuwanni a jihar.

“Yanzu a maganar da muke yi da kai dole ta sa ‘yan kasuwa sun fara yin addu’o’i domin kada aikin ya tabbata domin a gaskiya mutane na cikin damuwa tun da suka ji wannan hira da aka yi da Gwamnan a rediyo. Sannan kuma ga shi bai bayyana cewa, ga inda mutane za su koma ba idan ya rusa kasuwar.

ADVERTISEMENT

“Da ka shigo cikin Kasuwar zaka ga mutane na cikin damuwa kasantuwar basu ma san inda za su saka kansu ba kuma gashi babu tabbacin cewa idan an rusa Kasuwar wadanda kenan a yanzu za su sake samun shagonsu.” In ji shi.

Share