✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan kasuwar Olomore da aka harba basu mutu ba – Rundunar ‘Yan sanda

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta karyata jita-jitar da ake yadawa a kafafen sadarwa na zamani cewa, ‘yan kasuwar da jami’anta suka harba sun mutu.…

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta karyata jita-jitar da ake yadawa a kafafen sadarwa na zamani cewa, ‘yan kasuwar da jami’anta suka harba sun mutu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaidawa Aminiya cewa, ‘yan kasuwar su biyu na murmurewa a babban asibitin gwamnati da ke Idiyaba a Abeokuta, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar tare da mukarabbansa sun je duba majinyatan a asibitin inda suka tarar da su cikin yanayi mai kyau domin suna murmurewa sossai.

Ya ce, zuwa yanzu bincike ya yi nisa domin gano musababbin rikicin tare da hukunta masu hannu a ciki.

“Bai kamata a dinga yada labaran karya a kafofin sada zumunta a yanar gizo ba, irin wadannan bayanai da basu da tushe kan iya haddasa tarzoma.” in ji shi.

A ranar Alhamis din da ta gaba ta ne ‘yan sandan suka yi harbin kan mai uwa da wabi a kasuwar kayan gwari ta Olomore inda harsashi ya sami ‘yan kasuwar su mutum biyu, daya a kai daya kuma a kafa.

Daya daga cikin ‘yan kasuwar da aka harba

‘Yan sanda na sun farma wasu ‘yan kungiyar asiri ne, wadanda suka tsere masu sai suka yi yunkurin kame yaran mota da suke kwance a karkashin motocin su a harabar kasuwar lamarin da ‘yan kasuwar suka ce baza ta sabu ba, inda nan take ‘yan sandan suka fara harbin kan mai uwa da wabi.