Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

…’Yan kazagi ba za su iya hana Atiku aiki ba– Obasanjo

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya fadi a Legas, cewa ’yan Najeriya za su zabi Atiku Abubakar sosai.

Ya ce duk da cewa Atiku ba waliyyi ba ne, amma ya san cewa zai fi Buhari aiki, “Atiku zai kasance mai aiki tare da mutane, amma kuma ’yan kazagi ba za su hana shi aiki ba,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Obasanjo ya ce duk da cewa yana shan caccaka a kan matsayinsa game da Atiku da Buhari, yana nan a kan bakarsa

“Na yafe wa Atiku har zuciyata. Kuma duk wanda yake zargina da yafe wa Atiku, to na bar shi da Allah. Duk wanda ake nemi yafiya a wurinsa ya ki yafewa ba cikakken mai imani ba ne,’ inji shi.

ADVERTISEMENT

Obasanjo ya kara da cewa babu Shugaban Kasa a tarihin Najeriya da ya bar wa mataimainsa rikon gwamnatin kamar yadda ya yi lokacin da suke mulki.

“Kundin tsarin mulkin Najeriya a tsare yake. Babu bukatar sai sa sanar da haka. Ba sai na ce mataimakina ya ci gaba da gudanar da ayyukan mulki ba idan bana nan. Kawai idan Shugaban Kasa ba ya nan, dole kawai mataimakinsa ya ci gaba da aiki da cikakken iko. Kawai sai dai ya bukaci shawara a inda ake bukatar haka. Watakila kawai saboda ban taba barin kasar na kwana 104 ba, shi ya sa ba a san cewa Atiku ba yi rikon mulki ba,” inji shi.