✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Kungiyar IMN ba ’yan Shi’a ba ne – Sheikh Hamzah Lawal

Babban Sakataren Mu’assatut Thakafus Thakalain a karkashin Cibiyar Al-Thakalayn ta ’yan Shi’a a Najeriya, Sheikh Hamzah Muhammad Lawal ya ce Kungiyar IMN ta mabiya Sheikh…

Babban Sakataren Mu’assatut Thakafus Thakalain a karkashin Cibiyar Al-Thakalayn ta ’yan Shi’a a Najeriya, Sheikh Hamzah Muhammad Lawal ya ce Kungiyar IMN ta mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky ba ’yan Shi’a ba ne.

A cewarsa, akwai bukatar ’yan kasa musamman ’yan jarida da gwamnati da jami’an tsaro su fahimci bambancin da ke tsakanin akidar Shi’a da  Kungiyar IMN.

Sheikh Hamzah Lawal ya shaida wa Aminiya cewa “IMN kungiya ce ta harka, ma’ana kamar kowace irin harka ta neman canji da sauyi a kasa, ita kuma Shi’a akida ce.”

Ya bayyana cewa ya taba kasancewa dan Kungiyar IMN a 1980 zuwa shekarar 2000, shekara daya kacal da dawowarsa daga kasar Iran, inda ya je ya karanci fannin addini.

Ya bayyana takaitaccen tarihin yadda kungiyar IMN ta samu asali da cewa; “IMN ta faro ne a matsayin harkar tajididi ta siyasa da addini da kuma tattalin ariziki, wadda lokacin tana karbar irshadinta ne da shiryatarwa daga manyan malaman Sunnah na duniya, a kasashe irin su Masar da kuma Pakistan.

“Ta tsiro ne daga Kungiyar Dalibai, lokacin da aka haife ta sai ya yi daidai da lokacin juyin juya- hali na Jamhuriyyar

Musulunci ta Iran. Wannan ne ya bai wa Kungiyar

 

“Ta tsiro ne daga Kungiyar Dalibai, lokacin da aka haife ta sai ya yi daidai da lokacin juyin juya- hali na Jamhuriyyar Musulunci ta Iran. Wannan ne ya bai wa Kungiyar IMN misali mai rai, wanda take iya kallon abin da take tunani da cimmawa saboda haka ne ya sa ta zama kusa da salon siyasa na wannan juyin juya-hali na Iran a lokacin.

“A lokacin da kuma Shugaban IMN, wato Sheikh Ibrahim Zakzaky ya zama dan Shi’a sai ya shiga rudani na ko ya ci gaba da motsinsa na tajididi ko ya ci gaba da tajididin, amma ya ba shi fuskar Shi’a. Saboda haka harkar Sheikh Zakzaky kwado ce da cakude-cakude da mafarke-mafarke. Alal hakika idan aka bi diddigi tare da bincike na ilimi, za a ga cewa IMN ta fi kusa da Sunnah. Saboda haka ’yan jarida ya kamata su fara bai wa IMN sunan da suka bai wa kansu wato IMN,” inji shi.

“Muna son a lura da bambancin IMN da kuma Shi’a. IMN daban Shi’a kuma daban. IMN harka ce ita kuma Shi’a akida ce, don haka ba kungiya ba ce ta Shi’a,” inji shi.

Da aka tambaye shi game da mambobinta kuwa, sai ya ce “Eh, mafi yawa daga mabiyanta ’yan Shi’a ne, a lura da wannan amma akwai kuma da yawa daga cikin mabiyanta da suke ’yan Sunnah ne da kuma Kirista. Ya ce “Saboda haka ita harka ce kamar kowace irin harka ta neman canji da sauyi. Wadansu daga cikin shugabanninta na bayyana a cikin kaya irin na ’yan Shi’a amma iyakacinta ke nan. IMN ba ingantacciya ba ce, ita jabu ce, ita haja ce mara kyau wadda ba ma za a iya saida ta ba. Haja ce wadda take ba za a iya tallata ta ba.”

A kan batun kira da Al-Thakalayn ta yi, na cewa Gwamnati Jihar Kaduna ta saki Sheikh Zakzaky, sai ya ce “Abin da ya sa muke kira ga gwamnati ta saki Sheikh Zakzaky, muna ganin kila hakan zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a Jihar Kaduna da kasa baki daya. Wannan ne kawai dalilinmu na yin kiran.

“Amma sai dai abin tambaya an nan shi ne, me zai faru idan aka sake shi? Shawarata a nan ita ce, hakan ya kamata ya zama daya daga cikin babutuwan da za a tattauna. Dole a duba batun inda zai zauna idan an sake shi, shin zai koma Zariya ne, shin ’yan Zariya za su karbe shi, ko wasu makwabta ne za su amshe shi?

“Dole ne a duba wannan abin sosai kuma mu a shirye muke mu taimaka ko ba da gudunmuwa a wannan fanni. Haka kuma dole gwamnati ta damu a kan me zai faru idan aka sake shi. Wannan na daya daga cikin abin da ke damun gwamnati. Domin ba na tsammanin gwamnati ba ta son sakinsa amma suna ganin me zai biyo bayan sakinsa. Kowa na daga cikin masu ruwa-da-tsaki, don haka dole a hada kai hatta shi ma ya kamata ya kasance a cikin masu ruwa-da-tsaki,” inji shi.

A kan ko matakin gwamnati na soke Kungiyar IMN ne maslaha, sai ya ce ba ya tsammanin wannan mataki zai zama maslaha ga ayyukan ’ya’yan kungiyar. Ya ce akwai bukatar gwamnati ta zauna da su a tattauna yadda za a samu zaman lafiya.

Ya ce wannan kasar ta ’yan Najeriya ce baki daya, don haka a duba hanyoyin da suka dace domin samar da zaman lafiya amma ba ya ganin matakin gwamnati a matsayin  maslaha.

A kan ko suna da damuwa yadda lamarin rikicin ’yan Kungiyar IMN ke faruwa a kasar nan, sai ya ce “Hakika mun damu sosai domin muna ganin cewa idan ba a magance matsalar yadda ya dace ba, tana iya zama wata matsala da za ta koma irin ta Boko Haram amma da sunan ’yan Shi’a.”

Sheikh Hamzah Lawal ya hawarci kasashe irin su Iran da Masarautar Saudiyya su kauce wa yin katsalanda a Najeriya. Domin a cewarsa, zaman lafiyar Najeriya alhaki ne da ya rataya a kan kowane dan kasar nan. Ya ce bai dace ga Gwamnati Tarayya ta rika fifita wata kasa a kan wata kasar ba. Domin a cewarsa, dukkan Musulmin kasar nan dole ne su hada kai su kare martabar kasar nan.

Sai dai kuma a maraicen shekaranjiya Laraba, Mai magana da yawun Kungiyar IMN, Malam Ibrahim Musa ya fitar da takardar manema labarai, inda ya ce kungiyar tasu ta dakatar da jerin zanga-zangar da take gudanarwa.

Ya ce: “Harkar Musulunci a Najeriya (IMN) na sanar da jama’a da al’ummar duniya cewa ta dakatar da dukkan muzaharorin ‘Free Zakzaky’ na wucin-gadi don ba da dama ga sababbin kofofin warware takaddamar da ake ciki, musamman karar da lauyoyinmu suka shigar suna yin kule ga odar haramci da Gwamnatin Tarayya ta fitar a wannan mako.”