✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kwallon Nigerian Super Eagles biyar na daga cikin wadanda za su fafata a Gwarzon dan kwallon Afirka Ta Bana

A ranar Juma’ar da ta wuce ne Hukumar Shirya kwallon kafa a Afirka (CAF) ta zakulo ’yan kwallon 25 da za su fafata a gasar…

A ranar Juma’ar da ta wuce ne Hukumar Shirya kwallon kafa a Afirka (CAF) ta zakulo ’yan kwallon 25 da za su fafata a gasar Gwarzon dan kwallon Afirka ta bana.
Wata sanarwa da ta fito daga Hukumar kuma ta aika ga Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa NFF ta nuna daga cikin ’yan kwallon da ta zabo daga Najeriya akwai mai tsaron gida bincent Enyeama da Ahmed Musa da Emmanuel Emenike.  Sauran sun hada da ’yan kwallon tsakiya John Mikel Obi da kuma Sunday Mba.
Ana sa ran Hukumar CAF za ta sanar da dan kwallon da ya lashe gasar ce a ranar 9 ga watan Janairun 2014 a Legas a lokacin bikin cin abincin dare da kamfanin wayar sadarwa na GLO ya shirya.
Hukumar ta ce ta raba kyaututtukan gida biyu ne.  Na farko na ’yan kwallon da suka yi fice a harkar kwallo kuma suke gudanar da kwallo a wata kasa daban da tasu da kuma ta ’yan kwallon da suka yi fice amma suke wasa a kasashensu na asali.
Sunday Mba yana daga cikin ’yan kwallon da suka yi fice wadanda ke buga kwallo a gida.