Da Dumi Dumi

’Yan kwallon Southampton sun yi sadaka da albashinsu bayan an doke su 9-0

Dan qwallon Leicester City Jamie Bardy wanda ya zura qwallaye uku daga cikin tara da suka doke Southampton
Dan qwallon Leicester City Jamie Bardy wanda ya zura qwallaye uku daga cikin tara da suka doke Southampton

A ranar Litinin ce kulob din Southampton da ke Ingila ya bayar da sanarwar cewa daukacin ’yan kwallonsu da jami’ansu za su yi sadaka da albashinsu na wannan mako don tallafa wa mabukata bayan kulob din Leicester City ya lallasa su da ci 9-0 a gida a gasar Firimiya ta Ingila a ranar Juma’ar da ta wuce.

Kulob din ya dauki wannan mataki ne don ya zama darasi ga ’yan kwallon da jami’ansu kan abin kunyar da suka yi wajen kwasar kwallaye 9 a ragarsu ba tare da sun zura ko kwallo daya ba.

Wannan ne karo na farko da aka taba lallasa wani kulob da yawan kwallaye 9 a raga a gasar Firimiya ta Ingila.

An tafi hutun rabin lokaci ne da ci 5-0 amma abin mamaki sai aka kara wasu kwallaye hudu da hakan ya sa aka tashi wasan da ci 9-0.

Leicester City ta bi kulob din Southampton ne har gida, don ta yi mata lugudun kwallaye.

ADVERTISEMENT

Kawo yanzu kulob din Southampton ne na 18 a jerin kungiyoyin da ke fafatawa a gasar yayin da Leicester City ke matsayi na uku.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya