Search
Subscribe
’Yan majalisa za su gina hanya daga Gombe ta hade da Filato – Wase

Gwamna Inuwa Yahaya da Usman Bello Kumo da Alhaji Idris Wase suna mika wa daya daga cikin matasan babur

’Yan majalisa za su gina hanya daga Gombe ta hade da Filato – Wase

Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai Alhaji Ahmed Idris Wase, ya ce zai hada kai da dan majalisa mai wakiltar mazabar Akko Alhaji Usman Bello Kumo, don gina wata hanya da ta tashi daga garin Akko ta hade da Wase ta wuce Lantang ta hade da Wamba.

Alhaji Ahmed Idris Wase, ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen bikin raba kayayyakin jinkai da dan majalisar na Akko Alhaji Usman Bello ya yi wa al’ummar mazabarsa.

Ya ce Alhaji Usman Bello Kumo da aka fi sani da suna World mutum ne na mutane da kullum yake kwana ya tashi da al’ummarsa a ransa da tunanin yadda zai taimaka musu.

Ya kara da cewa irin wannan abin alheri da World ya yi wa al’ummarsa ya dace su sake ba shi dama idan zabe ya dawo a shekarar 2023 don sake darewa kan wannan kujerar saboda ya ci gaba da gudanar musu da ayyukan madalla na raya kasa.

A jawabin Gwamna Inuwa Yahaya, na Jihar Gombe ya jinjina wa Usman Bello Kumo ne bisa wannan kokari da yake yi ga al’umma da kuma yaba wa salon wakilcinsa.

Gwamna Yahaya, ya ce talakawa su ne gatan duk wani dan siyasa ba dan siyasa ba ne gatan talaka ba, saboda haka duk bai kamata dan siyasa ya wulakanta talaka ba.

Tun farko shugaban shirin Sanata Sa’idu Umar Kumo Garkuwan Gombe ya ce a wannan yanki ba su taba samun da da ya yi musu abin alheri irin Usman Bello Kumo ba, inda ya ce shi ma ya taba zama Sanata amma ba su samu kamarsa ba.

Sanata Kumo, ya ce za su ci gaba da bai wa Usman Bello Kumo duk wani hadin kai da goyon baya da yake nema don ya samu damar ci gaba da nemo musu ayyukan raya kasa ya kuma taimaki ’ya’yansu nan gaba.

Tsohon dan takarar Gwamna a Jam’iyyar APC, Alhaji Habu Mu’azu, kira ya yi ga ’yan siyasa su rika cika alkawari kamar yadda suke dauka a lokacin yakin neman zabe.

Alhaji Habu Mu’azu ya kara da cewa kada ’yan siyasa su rika cin zarafin wadanda suka zabe su, kamata ya yi su rika kamanta abubuwan da za a rika yaba musu.

Alhaji Usman Bello Kumo, ya ce shi yana ji a ransa al’umma sun gamsu da salon wakilcinsa don haka zai ci gaba da sauke nauyin da ke kansa.

Alhaji Usman Bello, ya yi kira ga ’yan siyasa su hada kai su zama tsintsinya madaurinki daya, inda ya ce hakan ne zai ba su damar zabar wanda ya kwanta musu a rai idan bai musu abin da ya kamata ba su yi korafi a kansa.

Kayayyakin da aka raba sun hada da babura 120 da kekunan dinki 150 da jannareta 50 da kuma tsabar kudi Naira dubu 20 ga mutum 400.

An gudanar da taron ne a kofar Fadar Mai martaba Sarkin Akko Alhaji Umar Muhammad Atiku da ke garin Kumo hedkwatar Karamar Hukumar Akko.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin