✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Majalisar Dattawa sun koka kan shingayen tsaro a Abuja

Yan Majalisar Dattawa sun koka kan yadda shingayen tsaron da sojoji suka kakkafa bayan harin Nyanya ke takura wa jama’ar da ke shiga ko fita…

Yan Majalisar Dattawa sun koka kan yadda shingayen tsaron da sojoji suka kakkafa bayan harin Nyanya ke takura wa jama’ar da ke shiga ko fita daga birnin Abuja.
A cewar ’yan majalisar mutane suna shan wahala matuka kafin su kai wuraren aiki ko gidajensu.
Sanata Solomon Ewuga daga Jihar Nasarawa ya ce damuwarsa ta farko ita ce yadda Najeriya a yanzu ta zama abin tsoro. Kowa na jin tsoron kowa domin ba ka san wanda yake rike da makami ba. Ya ce na biyu lamarin da ya faru a Abuja ya kawo damuwa kwarai fiye da yadda ake zato. Misali idan mutum ya fito daga Nasarawa da ya kawo Karu, to babu tabbacin lokacin da zai isa cikin Abuja.
Sanata Ewuga ya ce sojoji sun kafa shinge, “Ni kaina sai da na yi sa’o’i hudu da rabi a tsakanin Karu da Nyanya, abin da da minti ashirin zai kai ka. Idan aka ci gaba da samun jerin gwanon motoci haka, to abin da ka iya tasowa zai fi abin da ya riga ya faru muni,” inji shi.
Sanata Ibrahim Kabiru Gaya ya amince da bayanan Sanata Ewuga, inda ya ce shingen da jami’an tsaro suka yi ya sa mutane cikin damuwa. Ya ce kullum ka tashi da safe ba ka san yadda rayuwa za ta kasance ba. An sa mutane cikin halin tsoro. “Kana tafiya kana waiwayen bayanka, kullum maimakon a yi gyara sai kara jefa mutane cikin wahala ake yi,” inji shi.
Ya ce hanya mai layi biyar an mayar da ita layi daya. Abin da ya kamata a yi shi ne a sa sojoji biyar, wato soja daya a kan kowane layi. Idan soja ya ga wanda bai yarda da shi ba sai ya tsayar da shi.
Sanata Gaya ya ce idan an duba daga karshe ba wani abu suke yi ba. Wani zubin ma sai su karbi wani abu a hannun mutum. “Wannan kara wa jama’a da ke cikin zafi ne da wahala wani karin wahalar. Ana cikin talauci kuma an sake kara masu wani talaucin. Yanzu tafiyar minti talatin sai ka yi sa’o’i uku ko fiye. Sai a ga motoci 300 suna layi. Su ma motocin bama-bamai ne. Takurawar ta yi yawa. Lallai ne Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin saukaka wa jama’a,” inji shi.
Sai dai a wata takarda dauke da sa hannun Kakakkin Sojojin Najeriya Manjo Janar Chris Olukolade ya ba jama’a hakuri game da shingayen da aka sa. Ya ce matsalolin da jama’a ke fama da su yanzu na wani dan lokaci ne kafin a samu mafita ta dindindin.