✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan majalisar dokokin Jihar Nasarawa sun mayar da hannun baiwa “Mu ba almajirai ba ne,’’ inji Honorabul Muluku

Yan majalisar dokokin Jihar Nasarawa sun mayar wa Gwamna Almakura kyautar watan Ramadan da ya aika musu na buhun shinkafa da na sukari kowanensu. Shugaban…

Gwamna Umaru Tanko Almakura na Jihar NasarawaYan majalisar dokokin Jihar Nasarawa sun mayar wa Gwamna Almakura kyautar watan Ramadan da ya aika musu na buhun shinkafa da na sukari kowanensu.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Honorabul Godiya Akwashiki, wanda shi ne kuma shugaban kwamitin kula da jin dadin mambobin majalisar, ya shaida wa Aminiya cewa magatakardan majalisar ya karbi buhunan shinkafa da na sukari ya shigo da su zauren majalisa.
Kodayake shugaban masu rinjayen majalisar bai amince cewa ’yan majalisar dokokin sun mayar wa gwamnan kyautar ba, ya bayyana cewa ya dawo ke nan daga wata tafiya da ya yi zuwa Landan, saboda haka ba shi da cikakken labarin abin da ya faru. Sai dai a nasa bangaren, babban mataimakin Gwamna Almakura a kan ayyukan jinkai da tallafawa, Alhaji Safiyanu Rabi’u Garba, wanda shi ne kuma shugaban kwamitin da ke rarraba kyaututtukan Ramadan da Gwamna Almakura ya kafa, ya shaida wa wakilinmu cewa lallai an maida kayayyakin gidan gwamnati, bayan an kai su majalisar.
Ya ce, “Ba na nan a gari lokacin da abin ya faru. Abokan aikina ne suka kira ni ta waya suka bayyana min cewa kayayyakin da aka aika wa ’yan majalisar dokokin a matsayin kyautan watan Azumi daga wajen Gwamna Umaru Tanko Almakura, kamar yadda ya saba yi a kowane watan Ramadan, an dawo da su gidan gwamnati. Ban san dalilin da ya sa aka dawo da kayayyaki ba. Amma lallai an dawo da su gidan gwamnati”. Inji shi.
Wakilinmu ya tuntubi daya daga cikin ’yan majalisar dokokin wato Honorabul Alhaji Muhammed Muluku don jin ta bakinsa game da lamarin,  ya shaida masa cewa lallai an turo wa ’yan majalisar wadannan kyautan azumi daga Gwamna Almakura, amma sun mayar. Ya ce, “Kamar yadda ka sani, mu ’yan majalisa ba almajirai ba ne. Idan gwamnati za ta iya baiwa sarakunan gargajiya a jihar nan buhuna 5 na wannan kayayyaki kowanensu don mai za a ba mu buhu daya kowannenmu. Shi ya sa muka ga abin da ya fi dacew mu yi kawai shi ne mu mayar da kayayyakin. Ka ji dalilin ke nan”.
Ita dai majalisar dokokin Jihar Nasarawa ba karo na farko ba ke nan da take mayar wa Gwamna Almakura kyautar watan Ramadan, bara ma sun yi.