Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

‘Yan majalisar Kano ba su da hurumin binciken Ganduje -Kotu

A yau Alhamis babbar kotun da ke sauraran karar binciken Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje akan karban cin hanci, ta ce, ‘yan majalisar dokokin jihar ba su da hurumin binciken Gwamnan.

Alkalin kotun Ahmed Badamasi ne ya bayyana hakan lokacin da yake sauraran karar daga bangaren ‘yan majalisar da kuma kwamitin mutum bakwai da aka kafa na majalisar.

ADVERTISEMENT

Alkalin ya ce lokacin da mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jafar Jafar ya fara fallasa bidiyon da sun aika da shi zuwa hukumar ‘yan sanda ko EFCC ko kuma wata hukuma da ke alaka da su, su ke da hurumin binciken laifin cin hanci ba ‘yan majalisar ba.

ADVERTISEMENT