Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

‘Yan majalisar Kano sun amince da kirkiro masarautu 4

`Yan majalisar dokokin jihar Kano sun amince da bukatar kirkiro da sabbin masarautu hudu wadanda suka hada da: Bichi, Gaya, Karaye da Rano.

A yau Laraba ne ake saran kwamitin kananan hukumomin da harkokin masarautu za su gabatar da rahoton su game da bukatar kirkiro sarakunan masu daraja ta daya.

ADVERTISEMENT

Shugaban masu rinjaye na majalisar Baffa Babba Danagundi daga mazabar Kano Municipal ya gabatar da bukatar ga zauren majalisar. Kudurin dokar kirkirar sabbin masarautu ya tsallake karatu na farko a zauren majalisar, a yau majalisar za ta ci gaba da tattaunawa.

ADVERTISEMENT