✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Majalisar Nasarawa sun sake zaban Kakakin majalisar jihar

’Yan majalisar dokokin jihar Nasarawa (NSHA) a yau Litinin sun sake zaban Alhaji Ibrahim Balabare Abdullahi a matsayin  Kakakin majalisar. Sabon Kakakin Majalisar na wakiltar…

’Yan majalisar dokokin jihar Nasarawa (NSHA) a yau Litinin sun sake zaban Alhaji Ibrahim Balabare Abdullahi a matsayin  Kakakin majalisar. Sabon Kakakin Majalisar na wakiltar mazabar Umaisha da Ugya da ke jihar.

An zabi sabon Kakakin majalisar ne ta hanyar amincewar duk ‘yan majalisun, yayin da Akawun Majalisar Mista Ego Maikeffi Abashe, ya rantsar da Kakakin tare da Mataimakinsa Mista Tsetse Dandaura daga karamar hukumar Akwanga ta Arewa.

A jawabin Kakakin majalisar ya godewa sauran ‘yan majalisar da suka amince da zaban shi a matsayin Kakakin majalisar a wa’adi na biyu.