✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan majalisar Zamfara za su kirkiro masarauta

A yau Laraba ‘yan majalisar dokokin jihar Zamfara sun gabatar dokar kafa karin sabuwar masarautar Bazai. Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Alhaji Abubakar Gummi, ne…

A yau Laraba ‘yan majalisar dokokin jihar Zamfara sun gabatar dokar kafa karin sabuwar masarautar Bazai.

Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Alhaji Abubakar Gummi, ne ya karanta bukatar kafa sabuwar masarautar Bazai wanda za a cire ta daga cikin masarautar Shinkafi.

Majalisar ta gabatar da dokar daga darajar Hakimin Jangeru a gundumar Shinkafi zuwa sarki mai daraja ta uku da Hakimin Talata-Mafara, wato Kayayen Mafara.

Kanfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewa, majalisar ta kaddamar da kwamitin kirkiro da sabuwar masarauta wanda dan majalisa mai wakiltar Bungudu ta Gabas, Alhaji Ibrahim Kwatarkwashi zai jagoranta.