Da Dumi Dumi

’Yan PDP a Majalisa sun nemi tsawaita dokar zaman gida

Zauren Majalisar Wakilan Najeriya

’Yan Majalisar Wakilai na jam’iyyar PDP sun nemi gwamnatin tarayya da ta tsawaita dokar zaman gida a Yankin Babban Birnin Tarayya da jihohin Legas da Ogun na tsawon kwanaki 14, inda suka bayyana sassauta dokar a matsayin abin takaici da ba za su amince da shi ba.

A wani sako da shugaban su, Kinsley Chinda, ya rattabawa hannu, ’yan majalisar sun ce sassauta dokar zai kawo koma baya a yakin da ake yi da cutar coronavirus a kasar da kuma kara yaduwar cutar fiye da yadda ake tunani.

“A halin da ake ciki, lamarin yana barazana a jihohin Legas da Kano. Alkaluman da ake da su sun isa su nuna mana yanayin tsoro da damuwa da muke ciki.

“Mun kuma san cewa, gwamantin tarayya a karkashin Shugaba Buhari za ta kasa sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata na kare lafiyar ’yan kasar wanda yake kunshe a sashe na 14 karamin sashe na 2 na kundin tsarin mulki na shekarar 1999.”

’Yan majalisar wakilan na bangaren adawa sun kuma bukaci gwamnatin da ta tsawaita dokar daga ranar Litinin 4 ga watan Mayu.

ADVERTISEMENT

Sun yi kira ga gwamnatin da ta yi amfani da kwanakin da za ta kara ta rarraba kayayyakin kariya ga jama’a da kuma ba su tallafi kamar yadda ta yi alkawari.

Sun kuma bukaci a jawo jami’o’i da sauran cibiyoyin bincike wurin samo maslaha a yaki da cutar.

A sakon nasu, sun kara da cewa a tsawon makonni shida da fara yaki da cutar, babu wani tsari da gwamnati ta kawo saboda kula da kasuwanni, wuraren aiki da motocin haya.

“Akwai karancin kayayyakin kiwon lafiya. Jihohi da yawa ba su da cibiyoyin gwaji kuma ba su samu tallafi daga gwamnatin tarayya ba duk da makudan kudade da aka kashe zuwa yanzu daga kudaden da aka samu daga wasu masu hannu da shuni.

“Abu ne mai wahala a gane dalilin da ya sa gwamnatin tarayya ta sassauta dokar hana fita a yayin da cutar take ci gaba da yaduwa.”

Sakon ya jinjina wa gwmnatocin jihohi wadanda suka dauki tsauraran matakai saboda dakile yaduwar cutar.

Shugaba Muhammadu Buhari ne dai ya sanar da shirin gwamnati na sassauta dokar zaman gidan da aka kakaba da nufin hana yaduwar cutar coronavirus daga ranar 4 ga watan Mayu a wani jawabi da ya yiwa ’yan kasar a makon da ya gabata.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya