✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya 23 ke jiran hauni ya aike da su Lahira a Saudiyya

Hukumomin Saudiyya sun kare dokokin kasar bayan da aka rika cece-kuce kan fille kan wata ’yar Najeriya mai suna Kudirat Adeshola Afolabi da aka samu…

Hukumomin Saudiyya sun kare dokokin kasar bayan da aka rika cece-kuce kan fille kan wata ’yar Najeriya mai suna Kudirat Adeshola Afolabi da aka samu da laifin fataucin miyagun kwayoyi.

Yanzu haka dai akwai ’yan Najeriya 23 da suke jiran hauni ya aike da su Lahira a kasar ta Saudiyya, bayan samunsu da laifuffukan fataucin miyagun kwayoyi zuwa kasar.

Jakadan Saudiyya a Najeriya Ambasada Adan Mamoud Bostaji ya fadi a ranar Lahadin da ta gabata cewa, ana yanke hukunci kisa ne bayan an samu hujjoji da shaidu kan aikata laifi. Ya bayyana tsarin shari’a na Saudiyya da wanda ya ginu kan amana kuma yake aiki cikin gaskiya da adalci.

Jakadan ya ce akwai ’yan Najeriya kusan miliyan daya da rabi da suka zaune a Saudiyya ba tare da musgunawa ba.

Bostaji ya bukaci hukumomin da suke dukan filayen jiragen sama su rika aiki da tsare-tsaren da za su hana fataucin miyagun kwayoyi zuwa kasashen waje.

Wasu majiyoyi sun ce sun bankado wasu takardu da suke dauke da jerin sunayen ’yan Najeriya 23 da suke jiran hauni ya fille kansu.

Kuma Jakada Bostaji ya shaida wa wata kafar labarai cewa: “Ana yanke hukuncin kisa ne kawai bayan dukkan shaidu sun tabbata, kuma wannan shi ne abin da aka yi kan ’yar Najeriya da aka fille wa kai a baya-bayan nan.”

Ya kara da cewa: “Ko a bayanan baya-bayan nan da Babbar Mai tallafa wa Shugaban Kasa kan Harkokin Kasashen Waje da na ’Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje, Abike Dabiri-Erewa ta fitar ta yi Allah wadai da abin da matar ta aikata. Don haka ina fata gidajen watsa labarai da kafofin sada zumunta za su daina furta miyagun kalamai. Ina da yakinin dukkamu abin da muke so shi ne a yi adalci.”

Ya ce, ya kamata a fahimci akwai kyakkyawar dangantaka a tsakanin kasashen biyu ciki har da harkokin kasuwanci da mutunta juna a muhimman al’amuran da suka shafe kasashen duniya.

“Ina so in bayyana cewa akwai ’yan Najeriya nagari da suke zaune a Saudiyya kuma suna shiga a dama da su sosai a tsakanin al’ummar Saudiyya. Saudiyya ba ta da wata kullalliya da ’yan Najeriya. Yanzu haka akwai ’yan Najeriya miliyan daya da rabi da suke zaune a Saudiyya suna harkokinsu a kusan dukkan sassan tattalin arzikinmu. Wadannan ’yan Najeriya miliyan daya da rabi suna gudanar da halattattun ayyuka ba tare da ana musguna musu ba. Ba za ka fake da mugun aikin batagarin wadansu kalilan din ’yan Najeriya ba ka ce ana zaman doya da manja a tsakanin Saudiyya da Najeriya,” inji shi.

’Yan Najeriya 23 da suke jiran hauni ya aike da su Lahira bayan yanke musu hukunci kisa su hada da

Adeniyi Adebayo Zikri da Tunde Ibrahim da Jimoh Idhola Lawal da Lolo Babatunde da  Sulaiman Tunde da Idris Adewuumi Adepoju da Abdul Raimi Awela Ajibola da Yusuf Makeen Ajiboye da  Adam Idris Abubakar da Saka Zakaria da kuma Biola Lawal.

Sauran su ne: Isa Abubakar Adam da Ibrahim Chiroma da Hafis Amosu da Aliu Muhammad da Misis Funmilayo Omoyemi Bish da Misis Mistura Yekini da Amina Ajoke Alobi da Kuburat Ibrahim da Alaja Olufunke Alalaoe Abdulkadir da Fawsat Balagun Alabi da A’isha Muhammad Amira da kuma Adebayo Zakariya.

Takardar ta nuna cewa an kama ’yan Najeriyar ne da aikata laifuffukan da suka shafi keta dokokin safarar mayagun kwayoyi na Masarautar Saudiyya a karkashin Dokta mai Lamba M/39 ta ranar 8/7/1428 BH wadda ta tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da wannan laifi.

Wadannan ’yan Najeriya an kama su dauke da miyagun kwayoyi ne filayen jiragen sama na Sarki Abdul’aziz da ke Jeddah da na Yarima Muhammad bin Abdul’aziz da ke Madina lokacin da suka yi fasakwaurin miyagun kwayoyi ta hanyar suka hadiye a ciki a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017.