✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya 77 da ake zargi a Amurka: Gwamnati za ta ba Hukumar FBI hadin kai

A ranar 22 ga watan Agusta ce wani Babban Jojin Jihar California a kasar Amurka, Nick Hanna ya fitar da sunayen ’yan Najeriya 77 da…

A ranar 22 ga watan Agusta ce wani Babban Jojin Jihar California a kasar Amurka, Nick Hanna ya fitar da sunayen ’yan Najeriya 77 da ake zargi da aikata miyagun laifuka da suka shafi zamba cikin aminci ta yanar gizo.

Yanzu haka wadannan mutane sun bayyana a gaban kotun Amurka inda ake tuhumarsu kan aikata laifuka har 252 da ya sabawa dokar kasar Amurka.

Iro Balentine da Chukwudi Igbokwe su ne manyan wadanda ake zargi, inda sauran suka hada da Kingsley Umejesi, da Tityaye Igbokwe, da Ogedi Power, da Prince Chuddy, da Uche Nwanne da sauransu.

Tuni Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Birnin Washington na kasar Amurka, ya yi bayani game da kamen, inda ya yi Allah wadai da lamarin.

Mista Muhammad Suleiman, Babban Jami’i a Ofishin Jakadancin Najeriya da ke kasar Amurka, shi ne ya gabatar da wannan sanarwa a madadin jakadan Najeriya na kasar, Ambasada Justice Sylbanus Nsofor mai ritaya.

“’Yan Najeriya sun kasance mutane masu jajircewa da kuma kwazo, lamarin da ya sanya yake shawartar gwamnatin kasar Amurka a kan kada ta yi wa dukkan ’yan Najeriya jam’i ta hanyar bata sunansu baki daya saboda laifin wasu tsirarun mutane.”

A karshen sanarwar, gwamnatin Najeriya ta dauki duk kudirin bai wa gwamnatin Amurka hadin kai wajen gudanar da bincike da ya kamata.