Daily Trust Aminiya - ‘’Yan Najeriya masu gudun hijira a Nijar za su dawo gida’
Subscribe

Wasu ‘yan gudu hijira

‘’Yan Najeriya masu gudun hijira a Nijar za su dawo gida’

Gwamnatin Tarayya ta ba da tabbacin dawo da ‘yan Najeriya da ke gudun hijira a yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar gida.

Gwamnan Borno Babagana Zulum ya bayar da tabbacin a ziyarar gani da ido da suka kai wa ‘yan gudun hijirar tare da jami’an Gwamnatin Tarayya domin ganin shirin da ake yi na dawo da su gida.

Ya kai ziyarar ce tare da kwamishin hukumar kula da ‘yan gudun hijira na kasa, Basheer Garba Muohammed da kuma Ministar agaji, Sadiya Umar-Farouk wadda darakta mai kula da Ofishin Babban Sakataren Ma’aikatar, Ali Grema ya wakilta.

Sanarwar da ma’aikatar ta fita ta ce Zulum ya tabbatar wa ‘yan gudun hijirar aniyar Shugaba Buhari na ganin sun koma gidajensu.

Tawagar ta kuma tattauna da hukumomin Jamhuriyar Nijar wadanda Gwamnan Diffa, Isa Lameen ya wakilta.

Ta kuma kai ziyarar gani da ido a gidajen wucin gadi 1,000 da wasu 280 da ake gina wa ‘yan gudun hijira a garin Damasak na Jihar Borno.

texem
More Stories