✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya miliyan 10 sun yi ta’ammali da tabar wiwi a 2022 —NAFDAC

NAFDAC ta ce Najeriya ba za ta bari a halasta tabar wiwi ba.

Hukumar Kula da Inganci Abinci da Magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta ce mutane miliyan 10 da dubu dari 6 ne suka yi amfani da tabar wiwi a shekarar da ta gabata.

A cewarta, wannan adadi na wadanda suka yi ta’ammali da ganyen na wakiltar kaso 10.8 na al’ummar kasar.

Shugabar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana haka a yayin bikin kaddamar da rahoton Hukumar Kula da Amfani da Muggan Kwayoyi ta Duniya na shekarar 2022.

Ta ce, rahoton ya bayyana cewa tabar wiwi ce kwayar da aka fi amfani da ita, inda matsakaicin shekarun masu amfani da ita a cikin al’umma 19 ne.

Shugabar ta NAFDAC ta ce Najeriya ba za ta goyi bayan halasta amfani da tabar wiwi ba, duba da cewa ba ta da isassun kudaden da za ta yaki nomarta ba bisa ka’ida ba da kuma wuce makadi da rawa wajen amfani da ita.

Ta ce hakkin tabbatar da an yi amfani da tabar wiwi don samar da waraka ya rataya ne a wuyar hukumarta idan har aka halasta ta, kuma za ta yi wannan aiki ne tare da tabbatar da ba a karkata ta zuwa harkar shaye-shaye don maye ba.