Da Dumi Dumi

’Yan Najeriya sun soki ba shugabannin majalisa rigar kariya

Majalisar Wakilai ta sake bita kudirin da ke gabanta wsnda ya nemi a yi wa sashe na 308 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 gyara don a samar da dokar da za ta ba shugabannin Majalisar Dokoki ta Kasa kariya.

Sashe na 308 na kundin tsarin mulkin dai shi ne ya ba Shugaban Kasa da Mataimakinsa da gwamnoni da mataimakansu rigar kariya wadda ta hana a tuhume su a gaban kowace kotu a yayin da suke  kan mulki. Wannan kudiri da aka gabatar a Majalisar Wakilan don tattaunawa ya bukaci a yi wa wannan sashi kwaskwarima don a samar wa shugabannin majalisun biyu da mataimakansu rigar kariya.

Aminiya ta gano cewa wannan kudiri an gabatar da shi a karo na biyu bayan hawan Shugaba Buhari mulki, amma yana gamuwa da kakkausar suka da adawa daga jama’a. Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisa, Leo Ogor ne ya fara gabatar wa majalisar wannan kudiri wanda bai samu tagomashi daga jama’a ba.

Kudirin dai ya ci karo da doka ta biyar ta Tsarin Mulkin Jam’iyyar APC ta 2014, wadda a ta ce “A yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima don cire rigar kariya daga shugabannin da aka zaba wadanda ake tuhuma da aikata laifi.”

Sashi na 308 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ce: (1) (a) “Babu wata tuhuma da za a yi ko a ci gaba da yi wa wadanda suka shiga cikin wannan sashi a duk tsawon zamansu a kan mukamansu.”

ADVERTISEMENT

(b) “Haka kuma, “wanda yake karkashin wannan sashi, ba za a kama shi ba a kan wata tuhuma, ko kuma a tsare shi a gidan yari a kan umarnin wata kotu.”

(c) Ya ce “Babu wani zama ko umarni da wata kotu da zai bukaci wadanda suke karkashin wannan sashe su gurfana a gabanta ko a gurfanar da su .”

(3) Ya kawo cewa “Wannan sashi yana maganar masu rike ne da mukaman Shugaban Kasa da Mataimakin Shugaban Kasa da Gwamna da Mataimakin Gwamna, kuma yana maganar wadanda suke a kan mukamin a lokacin da suke a kan mukamin.”

A zaman da majalisar ta yi ranar Talata, a wannan karo dan majalisa Olusegun Adebunmi ne ya gabatar da kudirin a gaban majalisar.  Kuma Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Alhassan Ado Doguwa ya goya wa kudirin baya inda ya ce wannan kudiri ba wai shugabannin majalisar kawai ne zai amfana ba, a’a zai zama an yi shi ne saboda majalisar  baki daya.

Da yake tofa albarkacin bakinsa wani tsohon masanin al’amurran kasa, Cif Chekwas Okorie ya fada wa Aminiya cewa ’yan majalisar suna son su sanya wa kansu rigar kariya ce don su samu damar yin ‘ta’asa’.

“Wannan wani yunkuri ne da ’yan majalisar suke yi don ganin run lullube kansu da rigar kariya duk kuwa da yake sun san cewa ’yan Najeriya ba sa son haka.”

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa tsohon Shugaban Hadakar Jam’iyyu ta Kasa, Dokta Yunusa Tanko cewa ya yi wannan yunkurin da ’yan majalisar suke yi bai dace ba.

Shi ma da yake bayani ta wayar tarho, Farfesa Adam Anyebe, malami a Jami’ar Ahmadu Bello cewa ya yi “Su ne tushen matsalar da kasar nan take fama da ita. Tunda da ma sun yi kaurin suna game da rashawa, ka ga wannan yunkurin da suke yi wani sabon salo ne kawai na kokarin samun kariya daga mugun aikin da suke aikatawa.”

Haka shi ma Farefsa Auwalu Yadudu wanda masani ne a kan harkar shari’a ya nuna cewa wannan kudiri ya ci karo da ra’ayin jama’ar da suka zabe su don haka ba daidai ba ne.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya