Aminiya

’Yan qungiyar asiri 9 sun shiga hannu a Legas

Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas ta yi nasarar kama wadansu matasa 9 da take zargi da kasancewa ’yan qungiyar asiri a yankin Imota da ke Ikorodu, yankin da ya yi qaurin suna wajen ayyukan ’ya’yan qungiyar asiri.

ADVERTISEMENT

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas, DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa a ranar Juma’ar da ta gabata ce suka kama wadanda ake zargin bayan bayanan sirri da suka samu a kansu, inda da farko aka kama mutum biyu da suka hada da  Emmanuel Chinonso mai shekara 21 da Thomas Israel mai shekara 20, wadanda suka shaida cewa su jagorori ne a qungiyar asiri ta Eiye inda aka same su da wuqaqe da gatari da kuma hular qungiyar asiri, “Bayan jami’anmu sun kama mutum biyun, mun yi nasarar kama qarin mutum bakwai ta hanyar qara zurfafa bincike, mun kama su ne kwana uku da kama mutum biyun farko. Kuma za mu gurfanar da su a gaban kotu da zarar mun kammala bincike,” inji shi.

Unguwar Imota a Ikorodu a Legas yankin ne da ya yi qaurin suna wajen aikace-aikacen ’yan qungiyar asiri inda a shekarun baya da yawa daga cikin matasa ’yan qungiyar asirin suka bayyana tubarsu a gaban Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas da babban basaraken gargajiyar yankin.

ADVERTISEMENT