✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda masu karbar kudin beli tamkar masu garkuwa suke- Kwamishina

Kwamishinan ‘yan sandan Legas CP Zubairu Mu’azu ya bayya na cewa ‘yan sanda masu karbar kudin beli kafin su saki wadanda ake zargi da laifi…

Kwamishinan ‘yan sandan Legas CP Zubairu Mu’azu ya bayya na cewa ‘yan sanda masu karbar kudin beli kafin su saki wadanda ake zargi da laifi tamkar masu yin garkuwa da mutane dan karbar kudin fansa ne, domin duk mutumin da zai je ya kamo mutane ya tsare su, sannan ya ce sai an bashi kudi kafin ya sake su bashi da maraba da masu yin garkuwa da mutane dan a basu kudin fansa, ya ce beli kyauta ne bai kuma kamata a dan sanda ya karbi kudin beli ba.

CP Zubairu Mu’azu, ya bayyana haka ne a jiya a ofishin Hukumar da ke kula da miyagun laifuka daga Panti Taba inda ya kaddamar da dakunan bincike na zamani masu amfani da kimiyyar na’ura mai kwalkwalwa wajen bincike da yin tanbayoyi ga wadanda ake zargi da aikita laifuka .

Kwamishinan ‘yan sandan Legas Zubairu Muazu a lokacin da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki wanda ya gudana  jiya a Imota

Kana ya gabatar wa ‘yan jaridu wadanda ake zargi da aikata laifuka da dama cikin har da ‘yan kungiyar asiri 100 da aka kame su cikin kwanaki 7 kacal.

“Mu a Legas matsalar garkuwa da mutane ta fara zama tarihi, domin an dade ba a sami labarin haka ba duba da irin kokarin da muke, matsalar da muke tunkara ita ce ta ‘yan kungiyar asiri munyi nisa a shirye-shiryen da muke da kawar da matsalar kungiyoyin asiri”. In ji Kwamishinan ‘yan sandan Legas.

Hukumar ‘yan sandan tayi taron zaman lafiya na hadin gwiwa da Sarakunan gargajiya da iyaye da malaman makaranta da sauran masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaro a jiya a garin Imota da ke Ikorodu domin lalubo bakin zare nagance matsalar ‘yan kungiyar asiri inda a qarshen taron wata kungiyar maharba da mafarauta na yankin suka baiwa Hukumar kyautar namun daji da suka hadar da gada da berayen daji.

Dabobbin daji da mafarautan Ikorodu suka bai wa Hukumar ‘yan sandan Legas a Imota.

‘Yankin Ikorudu a Legas ya yi kaurin suna wajen aikace-aikacen ‘yan kungiyar asiri lamarin da ya sanya Hukumar ‘yan sanda ta mai da hankalin ta a yankin.