✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda na kama mu a wuraren da aka amince mu yi aiki – Masu Keke NAPEP

Masu tuka Keke-NAPEP a Abuja, sun zargi ’yan sanda da kama mambobinsu, a wuraren da Hukumar Kula da Lafiyar Motoci BIO ta yarje musu yin…

Masu tuka Keke-NAPEP a Abuja, sun zargi ’yan sanda da kama mambobinsu, a wuraren da Hukumar Kula da Lafiyar Motoci BIO ta yarje musu yin aiki.

Wadansu da Aminiya ta zanta da su a kusurwowin birnin inda daga can ne aka hana musu karasowa zuwa kwaryar Abuja, sun ce ’yan sandan na kama baburansu, sannan su bukaci Naira dubu biyu zuwa biyar, kafin bada belinsu.

A bangaren mahadar Kabusa da ke yankin Apo, jagoran masu sana’ar, Malam Yusuf Muhammad ya ce Hukumar BIO ta ba su damar yin aiki daga mahadar hanya da ta nufi garin Kabusa  zuwa unguwannin Galadimawa da Gudu da ke yankin Apo Abuja, yayin da suka hana su karasawa zuwa kusa da Unguwar ’Yan Majalisa da kuma hanyar da ta nufi Area 1.

“Amma duk da wannan damar da aka ba mu, sai ’yan sanda su kama baburanmu a tsakanin wadannan wurare, kuma ba su bada belin sai sun karbi Naira dubu biyu zuwa biyar,” inji shi.

Ya ce a ranar Juma’ar da ta gabata, sun yi rashin wani abokin aikinsu mai suna Mamuda Muhammad dan asalin Karamar Hukumar Sabuwa a Jihar Katsina, wanda ya yi fama da ciwon hawan jini kafin rasuwarsa.

Ya ce margayin ya ajiye aiki ne tun a wunin da ya gabaci ranar, bayan ya samu labarin ’yan sanda na kama mambobinsu da ke aiki a yankunan. Ya ce marigayin wanda ke kwana a cikin kekensa da yake ajiye ta a garejin babura da ke mahadar Kabusa, an same shi ba rai a cikin keken, inda hannuwansa da kuma kansa suka juyo ta kasa sannan kafafunsa kuma ke makale daga cikin keken jini na fito masa ta hanci da baki.

Ya ce bayan rasuwar marigayin sun sanar da ’yan sanda lamarin sannan suka zo garejin suka dauki hoton gawar tare da rubuta takarda a kai da ya ba su damar kai gawar garinsu inda aka yi masa jana’iza.

Wadansu masu sana’ar da wakilinmu ya zanta da su a yankunan Kado da Gwarimpa a Abuja, sun koka kan zargin musguna musu, inda suka yi kira ga hukumar da lamarin ya shafa ta sa baki.

Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Abuja, ASP Mariam Yusuf ta ce rundunarsu ba ta samu korafi daga masu Keke NAPEP ba, sai dai ta ce za su gudanar da bincike.