✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda na rikon sakainar kashi da kisan ’yata – Magidanci

Kusan wata biyu ne jama’ar Unguwar Jangwadu da ke daura da Kasuwar Alaba Rago suka wayi gari da alhinin kisan wata yarinya ’yar shekara shida…

Kusan wata biyu ne jama’ar Unguwar Jangwadu da ke daura da Kasuwar Alaba Rago suka wayi gari da alhinin kisan wata yarinya ’yar shekara shida da ake zargin wadansu matsafa suka sace suka kashe suka sace sassan jikinta inda suka binne ragowar jikin a gidansu. Lamarin ya sanya mutanen unguwar rushe gidan matsafan bayan gano gawar yarinyar da kasusuwan da ake zargi na mutane ne da daruruwan jakunkuna da kayan makarantar yara a gidan.

Mahaifin yarinyar Malam Idris Garba Lajawa ya shaida wa Aminiya cewa sama da kwana 50 ke nan da kashe ’yarsa, mai suna Walida wadda ita ce ’yarsa ta 13.

“Lamarin ya faru ne da yamma bayan Sallar Magariba mahaifiyarta ta tafi karbo markaden waken suya ta bar ta a kofar gida tana wasa, da ta dawo ba ta iske ta ba, sai ta kira ni a wayar salula ta shaida min, na tambaye ta ina ’yan uwanta? Ta ce sun tafi makaranta, haka muka bazama nemanta na kira malamai na shaida musu ana ta addu’a a nan da Arewa har gari ya waye,” inji shi.

Ya kara da cewa: “Wani abokina kuma malamina ya shaida min kada in damu yau za a ganta a raye ko a mace, haka kuwa aka yi bayan Sallar Asuba muka ci gaba da nema sai ga dan makwabciyarmu ya zo yana ce mana ya ga hannun Walida, ya ga jini kuma ya ga hantarta. To yaron karami ne a cikin yaranmu yake wasa don haka yana jin Hausa sosai nan take muka bi shi cikin gidan ya nuna mana inda aka binne ta. Ba mu taba zaton su suka dauke ta ba, inda muke nemanta daban inda muka gano ta daban yaron nan ya ci gaba da fadin abubuwa yana kwatanta wadanda suka kamo Walida. Sai mahaifiyarsa ta buge bakinsa ya yi shiru, a haka muka tone kabarin muka gano gawarta an sassare ta an kwashe kayan ciki da idanunta, an fasa kanta an kwashe kwakwalwarta, nan da nan aka sanar da ’yan sanda.”

Ya ce lokacin da ’yan sanda suka zo wajen baturen ’yan sandan yankin ya yi ta zubar da hawaye lura da halin da ya ga gawar ’yar tasa. “Baya ga gawarta an gano kasusuwan mutane da dama na yara da manya, an kuma gano kayan makarantar yara da suka hada da jakunkuna da rigunan ’yan makaranta da kayayyakin masu wanke takalma da sauran komatsan mutanen da ake zargi sun kama su sun kashe. A lokacin ’yan sanda sun kama matar suka tafi da ita, amma bayan kwana biyu ’yan uwanta sun je sun karbi belinta daga hannun ’yan sanda wanda hakan ne ya fusata jama’ar unguwar suka taru da shirin hallaka matar ’yan sandan suka sake tafiya da ita,” inji shi.

Ya ce, “Mutanen unguwar sun fusata ne domin an dade ana sace yaran unguwar akwai matar da aka sace mata ’yan biyunta, bayan faruwar lamarin. Mutanen unguwar na girmama ni sosai suna cewa lallai jinin ’yata yana da karfi domin a dalilinta ne asirin mutanen ya tunu.”

Ya ce “Tuni mutanen unguwar sun rushe kangon gidan wadanda ake zargin, babu abin da ya rage a ciki sai kabarin babansu mai suna Jangwadu shi ne asalin wanda ya asassa tsafi a gidan sunansa ne unguwar ta ci. An ce dalilin mutuwarsa ya sato wadansu yara ne a Unguwar Badagari asirinsa ya tonu jama’ar unguwar suka yi masa dukan kawo wuka lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa yau sama da shekara bakwai. Wannan matar ’yarsa ce akwai wani tela shi ma dansa ne wanda ya haifi yaro mai yin aski su ne suka kama min ’ya suka kashe amma sai ga su muna ganinsu suna yawo a gari  ba tare da an kama su ba.”

Ya ce a baya jikan Jangwadun da ke sana’ar aski an taba kama shi da kokon kan mutum a Unguwar Badagari inda daga baya aka sake shi aka ce yana da tabin hankali. “haka ita ma wannan matar ita ta baiwa mijinta guba ya sha ya mutu bayan an kamata ta kwashe shekaru biyar a gidan yarin sai aka sako ta aka ce wai tana da tabin hankali,” inji shi.

Malam Idris Garba Lajawa ya ce har yanzu gawar ’yarsa na hannun ’yan sanda wadanda suka ce suna yin bincike sai dai ya ce bai gamsu da yadda ’yan sandan suka yi wa lamarin rikon sakainar kashi ba, ganin ba su kama wadanda ake zargi ba, “Lamarin kisa ba karamin abu ba ne, a gidan da aka kashe min ’ya aka binne ta akwai coci ciki sannan ana karatun  boko da Nazare amma ba a kama mai makarantar ba, kuma  ba a kama masu jagorantar cocin ba. Hasali matar da aka kama sai aka sake ta daga baya, don haka nake kira ga mahukunta a bi min hakkin ’yata da aka kashe a tabbatar an hukunta masu laifi,” inji shi.

Wakilin Aminiya ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan  Jihar Legas DSP Bala Elkana kan lamarin, inda ya ce ba ya da masaniya a kan lamarin har zuwa lokacin da wakilinmu ya tuntube shi.