✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda na tuhumar marubuci ya nuna musu shaidani a jigon labari

Jami’an ’yan sanda, wadanda ke binciken wani marubuci a kasar Uganda, mai suna Norman Tumuhimbise, sun tursasa masa kan lallai ya nuna wanda yake nufi…

Jami’an ’yan sanda, wadanda ke binciken wani marubuci a kasar Uganda, mai suna Norman Tumuhimbise, sun tursasa masa kan lallai ya nuna wanda yake nufi da shaidan a littafinsa da ya rubuta, mai taken “Behind the Debil’s Line – A gefen shaidan” shi kuwa ya bayyana wa masu tuhumarsa kan lallai su karanta littafin, su gano da kansu. Wannan amsar da ya bayar  ba ta gamsar ba, don haka suka zarge shi da bata wa shugaban kasa suna.
A daidai lokacin da ’yan adawa ke yunkurin shirya gaggarumar zanga-zangar adawa da Musebeni, wasu kuwa rubuce-rubuce suke yi, inda suke raba littatafai, da nufin isar da sako ga mutane da ke tafiya a titi.
Musebeni ya kama ragama, ta hanyar juyin mulki tun a shekarar 1986, inda ya yi alkawarin kawo sauyi a siyasar kasar, a halin yanzu yana cikin jerin shugabannin Afirka da suka dade a kan mulki; kuma mai mulkin kama-karya ne da al’umma ta zuba wa ido.
“Shaidani da ake nufi dai shi ne shugaban kasa,” a cewar Tumuhimbise, wanda dan kungiyar adawa ne ta DCP, kamar yadda ya bayyana a makon da ya wuce. “Matukar Musebeni ya tsawaita mulkinsa, to yana kara zama nauyi ga kasar nan,” inji shi.
Wannan littafi na Tumuhimbise shagunan sayar da litrtattafai sun ki karbarsa, don haka ya dauki abinsa ya rika yawo ya talla da kansa, ko kuma ya bai wa wadanda suka amince za su sayar masa, shi kuwa ya ba su wani kaso na riba. Ya yi hakan ne don gudun kada gwamnati ta saye littattafai ta lalata su. A cikin littafin ya zargi Musebeni da “jiji da ki,” sannan ya kwatanta shi dad a tsohon Shugaban Libya marigayi Kanar Mu’ammar Gaddhafi.
Ofwono Opondo, wani mai magana da yawun gwamanti, ya bayyana littafin marubucin a matsayin furofaganda, wadda ba ta cancanci karatawa ba. Musebeni ya sake lashe zabe a shekarar 2011, yana shan suka, kan irin abubuwan da ya zargi tsohon shugaban kasar, wanda ya yaka. Wasu na zarginsa da kokarin kasancewa mai mulkin kasar iya rayuwarsa, sannan yana taimak wa masu cin hanci da rashawa, abokan huldarsa, alhali mafi yawan al’ummar Uganda na fama da talauci.